Albashin ma'aikata
Gwamnatin jihar Cross River ta amince da tsawaita hutu ga ma’aikatanta. An fara hutun kuma ana sa ran ma’aikata za su koma bakin aiki a shekara mai zuwa, 2024.
Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya amince da N100,000 a matsayin kyautar Kirsimeti ga ma'aikatan gwamnatin jihar. Kwamishinansa ya tabbatar da hakan.
A safiyar Lahadi aka fara jin cewa daga yau za a tafi yajin-aiki a Najeriya. Wannan sanarwa da ake ta yadawa karya ce kacokam kuma jama’a su yi watsi da ita.
Kungiyoyin kwadago sun yi barazanar shiga yajin aiki idan gwamnatin tarayya da jihohi suka ki biyan karin albashi da alawus na ma'aikata da aka alkawarta.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya amince da karin N35,000 a albashin ma'aikatan gwamnatin jihar, da alawus na kashi 50% na albashin Disamba.
Kana bukatar aikin taimakawa da aikace-aikace a ofishin jakadancin Amurka da ke Lagas Najeriya. Duba albashin da za a biya da ranar rufe neman aikin.
IPPIS ya jawo albashin ma’aikata fiye da 600 ya tsaya, ba za a cigaba da biyansu ba. Ma'aikatan ba su halarci tantancewar da aka yi domin gano ma'aikatan karya ba.
Ƙungiyar yan kasuwa (TUC) ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta biyan dukkanin ma'aikantan gwamnatin tarayya karin albashin N35,000.
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da biyan kudaden rage radadin cire tallafi na ma'aikata dubu 35 da aka fara a watan Satumba, kungiyar NLC ta yi barazanar yajin aiki.
Albashin ma'aikata
Samu kari