Albashin ma'aikata
Za a ji yadda kudin ma’aikata ya tashi daga N3000 a 1999 zuwa yau. Shehu Shagari ya fara kawo dokar mafi karancin albashi, kowa ya rika samun akalla N125 a wata.
Ministan kasafi da tsare-tsare, Abubakar Atiku Bagudu ya bayyana cewa kwata-kwata albashinsa bai kai ko miliyan daya ba inda ya ce mutane ne suke zarge-zarge.
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazak ya kafa kwamitin mutane 21 saboda mafi karancin albashin ma'aikata na N70,000 yayin da ake zanga-zanga.
Kungiyar Kwadago ta NLC a jihar Gombe ta bayyana rashin jin dadi kan kalaman Gwamna Inuwa Yahaya na jihar kan biyan mafi karancin albashin N70,000.
Gwamnan jihar Gombe ya fara fita zakka, ya ce ba zai iya biyan sabon mafi karancin albashi na N70,000 ba sakamakon karancin kafo da jihar ke samu daga tarayya.
Gwamnam jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da kwamitin da zai yi nazari kan mafi karancin albashin ma'aikata a jihar. Kwamitin ya kunshi manyan mutane.
Bola Tinubu ya yi alkawarin talaka zai sarara idan ya karbi mulki. Matsin rayuwa da zargin ko-in-kula sun yi sanadiyyar da matasa za su hau titi su yi zanga-zanga.
Gwamnatin Bola Tinubu ta dauki matakai a gurguje domin ganin ba ayi zanga zanga ba.Yayin da aka hango hadarin zanga-zanga, aka amince da kudirin karancin albashi.
Bayan amincewa da kudurin dokar sabon mafi karancin albashi da majalisa ta yi, an rika samun rade-radin cewa Shugaba Bola Tinubu na iya karawa 'yan NYSC alawus.
Albashin ma'aikata
Samu kari