Taraba
Bayan zarge-zargen Ɗan Bello kan Sheikh Abdullahi Bala Lau, mai kamfanin Fal-Damno a Taraba, Alhaji Ali Bukar Lau ya ce kamfaninsa ne ya yi aikin kwangilar.
Sanata Magatakarda Wamakko ya kafa kwamiti bayan wani mutum mai suna Musa Abubakar ya yi ridda saboda tsoron ’yan bindiga, ya sake karɓar addinin Musulunci.
Kakakin ‘yan sandan jihar Taraba, Abdullahi Usman, ya rasu da safiyar Lahadi. An shirya jana’izarsa da karfe 2 na rana a makabartar ‘yan sanda Jalingo.
Bayan kusan watanni uku ba a ganinsa a tarukan gwamnatin jihar Taraba, an fito da bayanai a kan dalilin rashin shigar mataimakin gwamna cikin jama'a.
Sanatan Taraba ta Kudu, David Jimkuta ya nuna ɓacin ransa kan hana jirgin saman da ya ɗauko sanatocin da ya gayyata sauka. Taraba, ya ce duk siyasa ce.
Rundunar 'yan sanda ta kama wasu 'yan bindiga masu garkuwa da mutane su 20. 'Yan sanda sun kai farmaki ne maboyar 'yan ta'addar a kusa da wata gona.
Ana shirin fara azumin 2025 kayan abinci sun yi sauki a kasuwanni Kano, Niger Taraba da jihohin Arewa. Farashin gero, wake, masara, shinkafa da dawa sun karye.
Jam'iyyar APC ta bukaci gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya bayyana wa al'umma wurin da mataimakinsa ya shiga tsawon watanni 3 ba a ji labarinsa ba.
Bayan shafe watanni uku babu labarinsa, al'umma a jihar Taraba sun bukaci sanin halin da mataimakin gwamna, Alhaji Aminu Alkali ke ciki game da lafiyarsa.
Taraba
Samu kari