Taraba
Kungiyar Kuteb Muslim Development Association (KMDA) ta yi magana kan zargin shirin rushe masallacin Juma'a inda ta shawarci Gwamna Agbu Kefas na Taraba.
Rundunar sojin Najeriya ta cafke mata da miji bisa zargin boye makaman yan bindiga a wani gida. Suna boyewa yan bindiga makami idan sun dawo daga kai hari.
Gwamnatin tarayya ta gargadi mutanen jihohi kan samuwar ambaliyar ruwa. Gwamnatin ta ce za a iya samun mummunar ambaliya a Kogi, Taraba, Neja da Benue.
Gwamnatin jihar Taraba ta karyata zargin da ake mata cewa tana shirin rusa gidan sarautar Takum da babban Masallacin Juma'a na garin, ta ce zargin ksrya ne.
Kungiyar ƴan Kabilar Kuteb KYN ta zargi gwamnatin Taraba da shirya rusa fadar Ukwe mai cike da tarihi da al'adu tare babban Masallacin Juma'a a garin.
Tsohon hafsan tsaro, Janar Theophilus Danjuma ya yi barazanar maka Fasto Paul Rika a kotu kan cin mutuncinsa a wani littafi da ya wallafa a watan Satumbar 2024.
Sojojin Najeriya sun kama manyan yan bindiga uku da suka fitini al'umma a jihohin Taraba da Filato tsawon shekaru. An kama wanda yake musu safarar makamai.
Kotun tarayya da ke Abuja ta ba da belin tsohon gwamnan Taraba a kan N150m. EFCC na zargin tsohon gwamnan da karkatar da kudi har N27bn a jihar Taraba.
Hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan Taraba, Darius Ishaku da Bello Yero a gaban kotu kan tuhuma 15.
Taraba
Samu kari