Siyasar Najeriya
Dan takarar jam'iyyar New Nigeria Peoples Congress, NNPP, Abba Kabir Yusuf, shine zababben gwamnan jihar Kano, ya yi nasarar kada Nasiru Gawuna na jam'iyyar APC
A labarin da ke iso mu, hukumar zabe ta INEC ta ce bata amince da sakamakon zaben majalisar wakilai da aka yi a jihar ba a ranar Asabar a yankin Takai ta jihar.
A halin yanzun INEC ta fara tattara sakamakon zaben gwamna a juhar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya, fafatawa ce tsakanin Kauran Bauchi da tsohon soja.
Za a ji cewa tun a jiya da safe kafin a sanar da wanda ya ci zaben Gwamnan Kano, ‘Dan takaran Jam’iyyar PRP ya hakura, Salihu Tanko Yakasai ya godewa jama'a
Hukumar zabe mai zaman kanta INEC tana shirin fara sakin sakamakon zabukan kananan hukumomi 44 na jihar Kano bayan yin zaben a jiya Asabar 18 ga watan Maris.
Za a samu matasa a majalisun dokoki, ‘Yan shekara 26 zuwa 30 sun yi nasara a Kwara, Yobe, Ogun, Shugaban majalisar Yobe ya rasa kujerarsa ga ‘Dan shekara 34.
Hukumar zabe ta ƙasa mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta gama tattara sakamakon zaben gwamna daga kananan hukumomin jihar Katsina guda 34, Dikko Radda da Lado.
Yadda sakamakon zaben gwamna ke fitowa daga jihar Gombe, da kuma dan takarar da ke kan gaba tsakanin Inuwa Yahaya da Muhammad Jibrin Dabarde na jam'iyyar PDP.
Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, na APC ya samu nasara kan babban abokin karawarsa na jam'iyyar PDP, Ladi Adebutu, a zaben gwamnan da aka kammala ranar Asabar.
Siyasar Najeriya
Samu kari