Rikicin PDP
‘Yan majalisar wakilai uku daga Kaduna sun sauya sheka daga PDP zuwa APC, yayin da Gwamna Uba Sani ya karrama su ta hanyar halartar zaman majalisar na yau.
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya fice daga PDP zuwa APC tare da kwamishinoni da tsohon gwamna Ugwuanyi, yana mai cewa PDP ta kasa sauraron muradun mutane.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bukaci mambobin jam'iyyar PDP da kada su karaya kan yawan ficewar da wasu ke yi. Ya ce jam'iyyar za ta farfado.
Gwamna Peter Mbah da dukkan majalisar zartarwarsa za su sauya sheka zuwa APC. An ce wannan zai zama sabon sauyin siyasa a Enugu da yankin Kudu maso Gabas.
Dan majalisar wakilai daga jihar Kaduna, Sadiq Ango Abdullahi, ya sanar da yin murabus dinsa daga jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya. Ya fadi dalilansa.
Gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya bada tabbacin cewa ba zai raba gari da jam'iyyar ba.
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya nuna damuwarsa kan sauya shekar da wasu ke yi daga jam'iyyar PDP zuwa APC. Ya ce ya damu matuka sosai.
Tsohon ɗan takarar PDP a jihar Zamfara, Mohammed Lawal, ya koma APC bayan ya zargi PDP da raina shi. Ya ce yana yarda da hangen nesan shugabannin APC.
Tsohon Mai Tsawatarwa a Majalisar Dattawa, Sanata Agboola Ayoola ya mika wasikar ficewarsa daga jam'iyyar PDP a jihar Oyo, ya ce zai canza akalar siyasa.
Rikicin PDP
Samu kari