Rikicin PDP
Jam’iyyar PDP ta rusa shugabanta a jihohin Akwa Ibom da Cross River, ta kuma nada kwamitocin rikon kwarya yayin da rikicin cikin gida suka jawo babban garambawul.
Sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya. Kawunan shugaban jam'iyya na kasa da sakatare na kasa sun rabu kan zabubbukan shugabanni.
Rahotanni masi tushe daga jihar Enugu sun bayyana cewa Gwamna Peter Mbah ya amince zai tattara kayansa da magoya bayansa daga PDP zuwa APC mai mulki.
Jam'iyyar PDP reshen jihar Abia ta ce Goodluck Jonathan na da cikakken hakkin tsayawa takarar shugaban kasa a 2027, amma sai ya bi tsarin jam’iyya da kundin kasa.
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya yi martani mai zafi ga ministan babban birinin tarayya Abuja, Nyesom Wike, kan sharuddan da ya gindaya ga PDP.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, tare da magoya bayansa a PDP sun gindaya sharuddan samun zaman lafiya a babbar jam'iyyar adawa.
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya gargadi babbar jam'iyyar adawa ta PDP kan dawo da Peter Obi. Wike ya ce dawo da Obi zai sa jam'iyyar ta sake shan kasa a 2027.s
Gwamna Bala Mohammed ya ce PDP ba za ta maimaita kuskuren da ta yi a 2023 ba wanda ya jawo mata faduwa zaben. Ya ce jam'iyyar na bukatar Kirista dan Kudu a 2027.
Gwamna Bala Mohammed, ya bayyana cewa akwai bukatar jam’iyyar PDP ta tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa daga Kudu, kuma Kirista don gudun maimaita kuskuren APC.
Rikicin PDP
Samu kari