Matasan Najeriya
An shawarci 'yan Najeriya da su fara tanadin abinci da rage kashe kudi yayin da ake shirin shiga shekarar 2024 wacce ka iya zuwa da matsin rayuwa.
Yar fafutuka a Najeriya, Aisha Yesufu, ta shawarci yan mata da su furtawa saurayi cewa suna sonsa da zaran sun ji ya kwanta masu ba wai su tsaya jira ba.
Tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Babangida ya bayyana cewa ya yi iya bakin kokarinsa a lokacin da yake kan karagar mulki tare da yi abokai a fadin Najeriya.
Gwamnatin Najeriya ta ce zata kara biyan magidanta mutum miliyan 4.5 tallafin N25,000 kowanensu a rukuni na biyu bayan rukunin farko na mutum 3.5m.
Wani matashi da ke zaune a Canada ya fallasa hanyoyi biyu da mutum zai bi ya tara dukiya a kasar ga wadanda ke shirin yin kaura. Ya ce siyan fili na ciki.
Kungiyar kwadago ta gargaɗi babban bankin Najeriya ya yi duk mai yiwuwa wajen ganin karancin Naira da ake fama da shi ya zo ƙarshe ko kuma ta shiga yaji.
Wani matashi dan Najeriya ya nunawa duniya makudan kudaden da aka yi kuskuren turawa asusun ajiyarsa na banki. Ya ce zai ajiye su a bankin har sai an kira shi.
Wata kotun majistire mai zama a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, ta garkame wani matashi da ya kashe mahaifinsa kan yana yi masa fada ba tare da aikata laifi ba.
Gwamnatin tarayya ta fara biyan masu cin gajiyar N-Power bashin kuɗaɗen da suka biyo na watanni, Dokta Betta Edu ta tabbatar da haka a wata hira ranar Alhamis.
Matasan Najeriya
Samu kari