Matasan Najeriya
Fitaccen Fasto a Najeriya, Abel Damina ya jawo ka-ce-na-ce bayan ya yi magana kan haramcin shan sigari ko giya a addinance inda ya ce ba zunubi ba ne ko kadan.
Rundunar 'yan sandan Kano ta bayyana nasarar damke wata matashiya, Shamsiyya Adamu da ta kware wajen satar wayoyin hannu tare da masu ba da gudunmawa.
NDLEA Kano ta kama mutane 1,345 da kwace 8.4kg na kwayoyi. Ta rushe sansanonin kwayoyi 20, ta gyara halin masu shaye shaye 101 da kuma hukunta 128.
Wani saurayi ya siya wa fitacciyar 'yar TikTok a Arewa, Maryam Sa'idu gida na N55m, ya ce ta daina zama a otel. Maryam ta ce ba za ta yi aure ba sai Tinubu ya sauka.
Wasu matasa a jihar Enugu sun zargi jami'an gwamnati da amfani da karfin gwamnati wajen nada sarki. Matasan sun tura takarda ga gwamnan kan lamarin.
An yada wani faifan bidiyo inda matashi ya bayyana nadamarsa kan rashin goyon bayan Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2023, yana mai cewa ya yi kuskure.
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya taya Buhari Sunusi Idris murna bisa nasarar lashe gasar Alkur'ani ta ƙasa da kashi 98.2. An ba Buhari kyautar kujerar aikin Hajji.
Tun daga rugujewar tushen wutar lantarki na kasa har zuwa rikicin sarautar birnin Kano, Legit.ng Hausa ta yi tsokaci ne kan abubuwa 10 da suka mamaye shekarar 2024.
Hukumar Kwastam ta Najeriya ta sanar da fara atisayen daukar ma'aikata a rukuni uku: Superintendent Cadre, Inspectorate Cadre, and Customs Assistant Cadre.
Matasan Najeriya
Samu kari