
Albashin ma'aikatan najeriya







Gwamnan Imo, Hope Uzodimma ya sanar da amincewarsa na fara aiwatar da sabon mafi karancin albashin N70,000 ga ma'aikatan jihar. Ya karawa wasu albashi.

Yan kwadago na barazanar tafiya yajin aiki a jihohin Katsina, Imo, Zamfara da Cross River a kan karin mafi ƙarancin albashi zuwa ranar 1 ga watan Disamba.

Gwamnatin Bauchi ta sanar da lokacin fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi a karshe watan Nuwamba. Bala Muhammad ya ce zai biya hakkokin ma'aikata a jihar.

Kungiyar 'yan kwadago a Zamfara ta yi barazanar tsuduma yajin aiki idan gwamnatin jiharba ta fara aiwatar da sabon mafi karancin albashi zuwa karshen Nuwamba ba.

Ministan Abuja, Nyesom Wike ya amince da biyan N70,000 ga ma'aikatan birnin Tarayya Abuja domin ragewa ma'aikatan halin tsadar rayuwa da ake ciki a Najeriya.

Fela Durotoye, tsohon hadimin Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa ya yi aiki a fadar shugaban kasa na tsawon watanni shida ba tare da an biya shi albashi ba.

Gwamnan Benue ya yi karin mafi ƙarancin albashi zuwa N75,000 ga ma'aikata. Gwamnan ya ce ya kara albashi sama da yadda Tinubu ke biya a matakin tarayya.

Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya yi magana kan dalilin jinkiri da aka samu kan fara biyan mafi ƙarancin albashi inda ya ce sai an gama tantance su.

Gwamnan jihar Plateau ya amince da sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatan jihar. Caleb Mutfwang ya amince a fara biyan ma'aikata sabon albashin N70,000.
Albashin ma'aikatan najeriya
Samu kari