Hukumar Sojin Najeriya
A taron da suka gudanar ranar Jumu'a a Kaduna, gwamnonin arewa 19 sun bada tallafin Naira miliyan N180 domin agaza wa mutane da harin sojoji ya shafa a Tusun Biri.
Rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta tabbatar da cewa dakarun Operation Hadarin Daji sun sheke yan ta'adda uku a wani samame da suka kai cikin dajin Sokoto.
Rundunar Operation Hadarin Daji ta samu galaba mai girma kan wasu manyan hatsabiban yan ta'adda a jihohin Zamfara da Sakkwato, ta kashe wasu daga ciki.
Malaman Musulunci daga Arewacin Nejeria sun yi ganawar sirri da Babban Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, kan harin da jirgin soja ya kai a Kaduna.
Gwamna AbdulRazaq na jihar Kwara ya ziyarci jihar Kaduna don yin ta'aziyyar mutanen da suka mutu a harin bam tare da ba da tallafin Naira miliyan 200.
Rundunar sojin kasan Najeriya ta ce ta samu nasarar fatattakar wasu 'yan bindiga daga dajin karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna, ta kwato makamai da babura.
Yan bindiga sun shiga garin Zurmi, hedkwatar ƙaramar hukumar Zurmi a jihar Zamfara, ana fargabar sun sace mutane 10 ciki har da mai jego da jaririnta.
An samu hatsaniya a sansanin horaswa na NYSC da ke Abuja bayan wani soja ya lakadawa dan NYSC duka tare da fasa masa wayar salula da kuma agogon hannu.
Wasu miyagun yan bindiga sun yi wa ayarin wasu motoci kwanton bauna a jihar Rivers. A yayin harin yan bindigan sun halaka sojoji hudu da direbobi biyu.
Hukumar Sojin Najeriya
Samu kari