Hukumar Sojin Najeriya
Majalisa ta yabawa ƙoƙarin rundunar sojoji inda kwamitin kudi ya gabatar da wani muhimmin kuduri don cire harajin kudin shiga na dakarun duba da yanayin ayyukansu.
Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaron da ke cikin ayarin Gwamna Babagana Umaru Zulum sun fatattaki ƴan Boko Haram da suka tare matafiya a Borno.
Rundunar tsaro ta dakile harin ramuwar gayya na ‘yan bindiga a Mada, karamar hukumar Gusau, jihar Zamfara inda ta yi nasarar hallaka hatsabibin dan ta'adda.
Mako guda bayan addabar wasu yankuna a jihar Kebbi, jami’an tsaro tare da hadin guiwar ‘yan sa-kai sun kawar da jagoran ‘yan kungiyar Lakurawa, Maigemu.
Yayin da sojoji ke kara matsin lamba kan yan ta'adda, wata mata da ake zargi da zama matar rikakken ɗan ta’adda ta yi bidiyo tana roƙon sojoji kada su kashe su.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wani fitaccen ɗan bindiga a jihar Katsina, Abu Radde da yaransa sun miƙa wuya ga jami’an tsaro inda suka saki mutum goma.
Wani tsohon babban soja a mulkin Janar Ibrahim Babangida Babangida ya Caccaki IBB bayan fitar kaddamar da littafin da aka yi a birnin Tarayya, Abuja.
Yayin da ake kokawa kan halin walwalar sojoji, Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar-janar Olufemi Oluyede, ya ƙara kuɗin ciyarwa daga N1,500 zuwa N3,000 a kullum.
Kungiyar ci gaban zaman lafiyabta matasa a Arewa maso Yamma, NWYPD ta yabawa salon jagorancin hafsan tsaro, Janar Christopher Musa a yaki da ta'addanci.
Hukumar Sojin Najeriya
Samu kari