Hukumar Sojin Najeriya
Yan bindiga sun tashi hankulan jama'ar wani yanki a jihar Kwara bayan miyagun sun kai wani hari a gidan Sarki inda suka sace ƴaƴansa guda uku yayin farmakin.
Majiyoyi sun ce karamar hukumar Safana a jihar Katsina ta kulla yarjejeniyar sulhu da ‘yan bindiga, kamar Jibia, Batsari, da Danmusa, domin zaman lafiya.
Yayin da ake ci gaba da yaki da ta'addanci a Najeriya, Sojoj sun gano gawarwakin fiye da 60 bayan luguden wuta kan ‘yan bindiga a Zamfara da ke Arewa maso Yamma.
Boko Haram ta kai kazamin hari Borno, inda ta kashe sojoji, sace ɗaliba, ƙone gidaje, shaguna da motoci wanda ya tilasta mazauna Kirawa tsere wa zuwa Kamaru.
Sojojin sama da na kasa sun kashe fiye da ’yan bindiga 100 a Zamfara tare da lalata babura, yayin da Operation FANSAN YANMA ke ci gaba da fatattakar su.
Hakimin Ɗan Isa ya tabbatar da cewa ƴan bindiga sun fara karɓar haraji kafin su bari a yi noma a daminar bana a kauyuka 35 da ke yankinsa a jihar Zamfara.
Wasu rahotanni sun tabbatar mana da cewa matashin soja ya daba wa ɗan sanda wuka har lahira a unguwar Mayo-Goyi, Jalingo da ke jihar Taraba a yankin Arewa maso Gaba.
Wasu tsofaffin sojoji sun mamaye hedikwatar ma’aikatar kudi a Abuja, suna neman a biyan alawus, giratuti da albashin da aka rike tun bayan barin aiki.
Gwamnati za ta dauki sojoji 13,000 aiki kafin ƙarshen 2025, amma rundunar soji ta ce tana fama da ƙarancin kuɗi, musamman wajen matsuguni da kayan aikin tsaro.
Hukumar Sojin Najeriya
Samu kari