NLC
Osita Okechukwu ya ce akwai hadari idan aka tashi mafi karancin albashi sosai, ya ce gwamnati tayi hattara, kul ta biyewa NLC wajen laftawa ma’aikata kudi.
Gwamnatin tarayya ta ba kungiyoyin kwadago na NLC da TUC tabbacin cewa za ta cika dukkan alkawurran da ta daukar masu a yarjejeniyar su ta 2023 don janye yajin aiki.
Kungiyoyin kwadago da suka hada da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa (TUC) sun shiga yajin aikin gargadi na kwanaki 14.
An ji cewa Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da cewa za a biya ma’aikata N10, 000 a rage radadin tsadar fetur. NLC ta ce wannan ya yi kadan a halin da ake ciki.
Shugaban ƙungiyar NLC na ƙasa, Joe Ajaero, ya bayyana cewa da yawan gwamnonin da aka sa a kwamitin mafi ƙarancin albashi ba su iya biya a jihohinsu.
An bar maganar N30, 000, NLC ta ce ya kamata mafi karancin albashi ya zama $300 ne a wata. 'Yan kwadago ba su yanke wani albashi ba, amma N200, 000 ya yi kadan.
Sanata George Akume ya sanar da za a rantsar da kwamitin karin albashi. Ranar Talata gwamnati za ta kaddamar da kwamitin da zai yi aikin karin albashin ma’aikata
Kungiyar TUC ta sake tura sabbin bukatu 10 ga Shugaba Bola Tinubu yayin da aka shiga sabuwar shekara inda ta ce dole ya aiwatar da su ko ya fuskanci matsala.
Kungiyar kwadago ta gargaɗi babban bankin Najeriya ya yi duk mai yiwuwa wajen ganin karancin Naira da ake fama da shi ya zo ƙarshe ko kuma ta shiga yaji.
NLC
Samu kari