Labaran tattalin arzikin Najeriya
Rahotanni sun nuna cewa neman wanda zai gaji kujerar Emefiele ta gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) yayi nisa. An lissafo wasu manyan mutane da ake zato.
'Yan Najeriya sun shiga tashin hankali, sun cike asusun sakon imel na CBN da sakwannin korafi game da halin da ake ciki na karancin kudi da kuma cire kudade.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya biya wasu daga kudaden da ake bin Najeriya bashi, ya sake cin wasu kudaden masu yawan gaske a shekarar da ta gabata ta 2022.
CBN ya bayyana cewa, zai fara aikin tabbatar da ya rufe duk wasu asusun banki a kasar nan da ba a hada su da BVN ba saboda wasu dalilai, ya bayyana meye yasa.
A dalilin canjin Naira da CBN ya yi, Gwamnati ta jawo Kamfanoni miliyan 25 sun mutu. Bayan tsawon makonni ba a san inda aka dosa ba, an dawo da tsofaffin kudi.
Masu sana'ar PoS da suka ci karen su babu babbaka a baya, yanzu sun zaftare kuɗin da suke caja a hannun mutane, yayin da aka samu wadatuwar kuɗaɗe a yanzu.
Bankuna sun fara kokawa kan yadda 'yan Najeriya suka daina kawo kudinsu a ajiye musu a wannan lokacin bayan barkewar karancin kudi da aka samu a baya-bayan nan.
Zababben gwamnan jihar Katsina Radda ya bayyana shirinsa idan aka rantsar dashi a matsayin gwamnan jihar Katsina a watan Mayu da ke tafe nan ba da jimawa ba.
Jihar Gombe ta zo ta ɗaya a cikin jerin jihohin da ake gudanar da harkokin kasuwanci cikin sauki a tarayyar Najeriya. Wani sabon rahoto da aka saki ya nuna haka
Labaran tattalin arzikin Najeriya
Samu kari