Mai Deribe: Mamallakin Fadar Zinari a Najeriya Da Ke Saukar Manyan Shugabannin Duniya

Mai Deribe: Mamallakin Fadar Zinari a Najeriya Da Ke Saukar Manyan Shugabannin Duniya

  • Marigayi Mai Deribe yana daya daga cikin hamshakan attajiran Najeriya da suka mori dukiyarsu a duniya
  • Deribe ya gina fadar Zinari a Maiduguri wacce ta dauka magina shekaru 10 suna aikinta kafin su gama
  • Daga cikin manyan shugabannin da suka ziyarci fadar Deribe, akwai tsohon shugaban kasar Amurka, George Bush da Olusegun Obasanjo

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Babu shakka marigayi Alhaji Mai Deribe na daya daga cikin hamshakan masu kudi a Najeriya a karni na 20.

Ya gina gidansa da sirkin kumfar Zinari sannan ya mallaki jirgin sama nashi na kansa.

Kamar yadda Northeast Reporters suka wallafa, irin jirgin samansa mutum 12 ne kacal a duniya suka taba mallakarsa.

Ginin gidansa mai suna 'Gidan Deribe' ya dauka hankalin jama'ar duniya.

Babu shakka kuwa, don gidan ya bai wa kusoshi a duniya masauki kamar su Yarima Charles na kasar Birtaniya da marigayiyar matarsa, Gimbiya Diana.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Dawo Najeriya, Gbajabiamila da Ganduje Sun Tarbo Shi a Filin Jirgi

Wadanda suka taba shiga mashahuriyar fadarsa sun hada da tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo, Sarki Juan Carlos na kasar Spain da kuma tsohon shugaban kasar Amurka, George Bush.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An kaddamar da ginin Gidan Deribe ne a yayin mulkin soji, zamanin tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida, wanda shi ya zama mai masaukin baki a fadar zinarin.

Babu shakka an gano cewa, marigayin attajirin ya kashe dala miliyan 100 a kan ginin yayin da duk wata ake kashe dala miliyan biyar don tsaftacesa.

Mai Deribe: Mamallakin fadar zinari a Najeriya da ke saukar manyan shugabannin duniya
Mai Deribe: Mamallakin fadar zinari a Najeriya da ke saukar manyan shugabannin duniya. Hoto daga Northeast Reporters
Asali: UGC

Deribe ya kwashi shekaru 12 a cikin gidan kafin ya rasu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, gidan yana da sassa daban-daban tare da rukunin dakunan bacci biyar-biyar har kashi hudu ga kowacce daga cikin matansa.

Dan sa, Shettima Abubakar Deribe ya tabbatar da cewa an kwashe shekaru 10 ana aikin ginin fadar ba tare da tsayawa ba.

Kara karanta wannan

Obasanjo, Buhari, IBB Da Lokuta 9 Da Shugaban Najeriya Ya Zama Shugaban ECOWAS

Wani kamfanin kasar Italiya mai suna Giovanni Monzio Compagnoni ne ya zuba wa gidan kayayyakin bukata da suka hada da kujeru, gadaje da kayan madafi.

Shettima ya kara da cewa, kofar shiga gidan harsashi baya huda ta.

An haifa marigayi Mai Deribe a shekarar 1924 kuma ya rasu a shekarar 2002 a garin Makka da ke kasar Saudi Arabia. Ya rasu ya bar 'ya'ya 27.

Asali: Legit.ng

Online view pixel