Labaran tattalin arzikin Najeriya
Majalisar dattawa ta amince da bukatar karbo bashin $21bn daga kasashen waje da Shugaba Tinubu ya nema. Wasu Sanatoci sun nemi a fayyace amfanin bashin ga al’umma.
Shugaban kamfanin BUA, AbdulSamad Rabiu ya bayyana cewa nan gaba farashin kowane buhun siminti zai sauka a Najeriya idan darajar Naira ta ƙara tashi.
Najeriya ta karbi wasu kasashen Afrika a Abuja domin halartar taron makamashi da NMDPRA ta fara na kwana biyu. Shugaba Bola Tinubu ya nemi hadin kai.
Jagoran jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya isa fadar shugaban kasa domin halartar taron tattalin arziki a Abuja. Ana sa ran Bola Tinubu zai je taron.
Yayin da ake cigaba jimamin mutuwar Muhammdu Buhari, tsohon shugaban kungiyar kwadago, Ayuba Wabba ya bayyana babban rashi da aka yi bayan rasuwar dattijon.
Duk da cewa an kashe makudan kudade, amma rashin aiwatarwa da ingantaccen tsari ya hana shirye-shiryen Buhari magance talauci da samar da aiki yadda ya kamata.
Matatar Dangote ta rage farashin man fetur a fadin Najeriya zuwa N820 daga N840. Sauke farashin fetur ya biyo bayan saukar farashin danyen mai a duniya.
NBS ta ce farashin gas ya ƙaru a Mayu: 5kg ya kai N8,167.43, 12.5kg ya kai N20,709.11. NBS ta ce gas din ya fi tsada a Abia yayin da ake samunsa da araha a Oyo/Yobe.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce zuwansa mulki Najeriya na neman durkushewa amma ya ceto kasar da tsare tsaren da ya kawo. Ya ce ya gaji tattali maras inganci.
Labaran tattalin arzikin Najeriya
Samu kari