Hukumar Jin dadin yan sanda
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta gudanar da ranar 'yan sanda ta farko a Najeriya. An gudanar shara, raba tallafin magani da duba marasa lafiya a jihohin Najeriya.
Dakarun rundunar 'yan sanda sun ceto mata 5 a Kankara da wasu 2 a Malumfashi da ke jihar Katsina bayan fafatawa da ‘yan bindiga, an mayar da su gida lafiya lau.
Jami’an ‘yan sanda sun harba barkonon tsohuwa tare da fatattakar masu zanga-zanga a Fatakwal, jihar Rivers inda suka kuma doki wasu ciki har da ‘yan jarida.
Rundunar ‘yan sandan Kano ta cafke Usman Sagiru mai shekara 20 daga Sharifai kan zargin kashe wani dan sa-kai da harin da aka kai bayan sallar idi a Kano.
Kakakin ‘yan sandan jihar Taraba, Abdullahi Usman, ya rasu da safiyar Lahadi. An shirya jana’izarsa da karfe 2 na rana a makabartar ‘yan sanda Jalingo.
‘Yan sanda sun kama masu safarar makamai, miyagun kwayoyi da jabun kuɗi a samame daban-daban, inda suka cafke masu hannu a laifuka tare da kayayyakin haram.
Rundunar ‘yan sanda ta Rivers ta musanta cewa an kai hari kan gidan Nyesom Wike, tana mai cewa rahoton ba gaskiya ba ne, don haka jama’a su yi watsi da shi.
Yayin da ake ci gaba da shari'a kan zargin samun makudan kudi a asusun Abba Kyari, Iyalansa sun karyata zargin yana da asusun banki guda 10 da N200m.
Gwamnatin Kano ta ce ba za ta zuba ido a rika amfani da tashe ana tayar da hankula a jihar ba, kuma tuni kwamitin tsaron da aka kafa ya fara hana karya doka.
Hukumar Jin dadin yan sanda
Samu kari