Hukumar yan sandan NAjeriya
Sanatar Kogi ta Tsakiya da majalisar dattawa ta dakatar, Natasha Akpoti Uduaghan ta bayyana cewa babu gaskiya a labarin cewa ta fasa zuwa gida hutun Sallah.
Gwamnan Edo, Monday Okpebholo ya bayyana matukar takaici a kan yadda mutanensa suka yi wa wasu 'yan Kano da suka ratsa ta jiharsa a hanyarsu ta dawowa gida.
Direban motar da ta dauko mafarauta 'yan Arewa da aka kashe a jihar Edo ya fadi yadda 'yan sa-kai suka tare su tare da hallaka da dama daga cikinsu.
Kungiya ta soki Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi bisa kin bin umarnin 'yan sanda, wanda ya janyo mutuwar mutane da dama.
Bayan kammala sallar idi a Gombe, rahotanni sun tabbatar da cewa an samu turmutsutsu yayin da yara biyu suka rasa rayukansu sannan wasu 20 suka jikkata.
Rundunar ‘yan sandan Katsina ta cafke wani mutum, Alhaji Surajo Mai Asharalle da wasu uku kan zarginsu da kai wa jami’an Hisbah hari, inda suka jikkata su.
Mai martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya goyi bayan matakin da jami'an tsaro suka dauka na hana gudanar da hawan Sallah a wannan shekarar.
Bayan kisan wasu ƴan Arewa fiye da 16 a Uromi da ke jihar Edo, a yau Asabar 29 ga watan Maris aka birne wasu daga cikinsu bayan samun gawarwakinsu.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira daga mummunan nufin mutanen Uromi, Ɗayyabu Yahaya ya bada labarin abin da ya faru har aka kashe ƴan uwansa a jihar Edo.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari