Hukumar yan sandan NAjeriya
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sauke Solomon Arase daga shugabancin hukumar jin daɗin ƴan sanda ta ƙasa (PSC), ya maye gurbinsa da Hashimu Argungu.
Wasu miyagun ƴan bindiga sun yi awon gaba da fasinjojin motar Bas waɗanda suka taso daga jihar Enugu da nufin zuwa babban birnin tarayya Abuja a Nasarawa.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP) a zaben 2023, Peter Obi ya yi Allah wadai da kisan da aka yiwa jami'an 'yan sanda a jihar Zamfara.
Rundunar 'yan sandan Najeriya hadin gwiwa da mafarauta daga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun fatattaki wasu sansanin 'yan ta'adda da su ka addabi Abuja.
Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da cewa jami'anta sun samu nasarar hallaka wasu 'yan bindiga mutum uku a jihar Katsina a yayin wani artabu.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hare-haren ta'addanci a wasu kauyukan karamar hukumar Shiroro cikin jihar Neja. Sun hallaka mutum bakwai har lahira.
Wasu tsagerun ƴan bindiga sun kai hare-haren ta'addanci kan mazauna kauyuka 13 a yankin ƙananan hukumomin Safana da Dutsinma a jihar Katsina ranar Talata.
Yadda wasu direbobin kasar nan ke awon gaba da wasu jami'an tsaro idan an tsare su a hanya ya fara ci wa rundunar 'yan sandan kasar nan tuwo a kwarya.
Tun bayan zargin cewa mutuwar mawaƙi Mohbad ba ta Allah ba ce, gwamnati ta dora alhakin binciko dalilin mutuwar a wuyan asibitin koyarwa na jihar Lagos, (LASUTH).
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari