Jihar Nasarawa
A ranar Litinin 2 ga watan Oktoba, Kotun zaɓe ta sauke gwamna Abdullahi Sule kana ta ayyana ɗan PDP a matsayin sahihin wanda ya lashe zaben gwamnan Nasarawa.
Kotun sauraran kararrakin zaben a Nasarawa ta rusa zaben Gwamna Abdullahi Sule inda ta tabbatar da David Ombugadu na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zabe.
Yan bindiga sun harbi dalibai uku sannan suka sace wata daliba a Kwalejin Kimiyya da fasaha ta Isa Mustapha Agwai da ke garin Lafia a Jihar Nasarawa.
Wani magidanci, Mista Williams ya shiga hannu bisa zargin yana da hannu a mutuwar ɗiyarsa 'yar shekara 12 ta yanayi mai ban tausayi a gonarsa a Nasarawa.
Kotun zabe mai zama a Lafia babban birnin jihar Nasarawa ta gama sauraron kowane ɓangare, ta shirya yanke hukunci kan zaben gwamna Abdullahi Sule na APC.
Jami'an hukumar tsaron farin kaya (DSS) sun damƙe wasu ma'aikata bisa zargin wawure kayayyakin da gwamnati ta ware domin tallafa wa yan ƙasa su rage radadi.
Majaliaar dokokin jihar Nasarawa ta aike da sakon jaje ga iyalan mutum 12 da suka rasa rayuwarsu sakamakon haɗarin jirgin ruwa a yankin karamar hukumar Lafia.
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya raba sabbin mukaman ministoci a ranar Laraba 16 ga watan Agusta, Imaan Sulaiman Ibrahim na daga cikin wadanda su ka samu mukamin.
Masu garkuwa da mutane sun sace basaraken garin Gurku da ke karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa, Jibril Mamman Waziri, da matarsa, Hajiya Sa’adatu Waziri.
Jihar Nasarawa
Samu kari