Manyan Labarai A Yau
A cikin jihohin Najeriya 36 da ake da su, akwai wadanda suka fi sauran yawan fadin kasa. Daga ciki mun tattaro muku jihohi 13 wadanda suka fi yawan fadin kasa.
Tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da wasu sufetocin yan sanda uku tare da sace makamansu a garin Ohoror da ke karamar hukumar Ughelli ta arewa, jihar Delta.
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama masu adaidaita sahu kimanin 52 a sassa daban-daban na jihar bisa aikata ayyukan badala da suka hada da askin banza.
Shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Asabar, ya yanke shawarar halartan bikin rantsar da sabon gwamnan Kogi, Usman Ododo ta yanar gizo daga kasar Faransa.
Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya gargadi masu yi wa masu garkuwa da mutane, yan bindiga da sauran miyagu leken asiri a Abuja da su tuba ko su mutu.
Mataimakin gwamnan jihar Kogi, Salifu Oyibo, ya dauka hankalin yan Najeriya a soshiyal midiya yayin da bidiyonsa duke a gaban tsohon gwamna Yahaya Bello ya yadu.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nuna halin dattako yayin da suke hanyar tafiya da ayarin motocinsa. Gwamnan ya sauko ya ba wata da suka buga wa mota hakuri.
Gwamnatin jihar Kano ta gargadi shugabannin kananan hukumomin jihar kan sayar da kadarorin gwamnati ba bisa ka'ida ba a jihar ko su fuskanci hukunci.
Jim kadan bayan rantsar da shi a matsayin sabon gwamnan jihar Kogi a ranar Asabar, 27 ga watan Janairu, Usman Ahmed Ododo ya nada mambobin majalisarsa.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari