Manyan Labarai A Yau
Wata babbar kotun jihar Rivers ta bayar da sabon umarni ha rundunar ƴan sandan Najeriya kan yunƙurin cafke shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Rivers.
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC), ta bankado wata kungiyar addini da ke taimakawa barayi wajen karkatar da kudaden sata.
Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya yi magana kan shirin mayar da hedikwatar hukumar FAAN daga babban birnin tarayya Abuja zuwa Legas.
Pelumi, matashiyar budurwa ‘yar Najeriya da ta dauki haramar tuko mota daga Landan zuwa Legas ta nunawa mutane abubuwan da cikin motarta ya kunsa. Harda wajen bacci.
Tawagar 'yan wasan Najeriya ta Super Eagles za ta samu kyautar N2.24bn idan ta doke tawagar Palancas Negras ta Angola a wasan daf da na kusa da na karshe.
Shugaban ƙungiyar gwamnonin yankin Arewa maso Yamma, Dr. Dikko Umar Radda, ya bayyana cewa babu batun yin sulhu tsakaninsu da ƴan bindiga a yankin.
Sanata Shehu Sani ya ce bai kamata yan Najeriya su yi martani ba illa ihun amin ga hasashen Fasto Enoch Adeboye na cewa naira za ta kara karfi kan dala.
Wani bam da ƴan ta'addan Boko Haram suka dasa ya tashi da wasu mutane a jihar Borno. Bam ɗin dai ya yi sanadiyyar halaka mutum 12 yayin da wasu suka jikkata.
Majalisar wakilai ta dauki mataki domin kawo karshen rikice-rikicen da suka addabi jihar Plateau. Majalisar ta kafa kwamitin da zai gano musabbabin rikicin.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari