Manyan Labarai A Yau
Sarkin Ilorin ya bayyana cewa faifan bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda yake nuna ana zanga-zanga a fadarsa ba gaskiya. Ya bukaci ayi watsi da shi.
An sha wata ‘yar dirama a kan titi yayin da wani fasto ya zo yana kokarin dawo da hankalin wani mahaukaci ta hanyar yi masa addu’a. Mahaukacin ya fafata da faston.
An shiga jimami bayan aukuwar wani mummunan hatsarin mota a jihar Ondo. Mutum hudu sun rasu yayin da wasu mutum 10 suka samu raunuka daban-daban.
Sanata Shehu Sani ya yi Allah wadai da fitowar da wasu dattawan mata suka yi a titi babu kaya da sunan zanga-zanga kan tsadar rayuwar da ake ciki.
Wasu rubuce-rubuce da aka yi a shafin Facebook sun yi iƙirarin cewa hamshakin attajiri a Najeriya, Femi Otedola yana bayar da kyautar kudi. An gano gaskiya kan hakan
Jigon jam'iyyar PDP, Segun Showunmi, ya bayyana cewa 'yan Najeriya bai kamata su dawo da jam'iyyar APC ba kan mulki duba da wahalar da aka sha a baya.
Wasu tsagerun ‘yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun farmaki garuruwa a karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna. Sun kashe mutum 9 tare da sace 35.
Sanata Shehu Sani ya nuna damuwa kan rashin samun wutar lantarki sosai yayin da gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu ta bayyana yunkurinta na cire tallafin lantarki.
Goodluck Jonathan, tsohon shugaban kasar Najeriya, ya nemi 'yan Najeriya su taya mahaifiyarsa addu'a saboda damuwa da ta shiga bayan rasuwar yayansa.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari