Manyan Labarai A Yau
'Yan siyasa sun yi suna wajen shirga karya, ana kokarin kawo karshensu. IPC ta ba ‘yan jarida horo na musamman a kan bankado bayanai da labaran bogi.
Azumin watan Ramadan na shekarar 2024 zai fara ne a ranar Litinin, 11 ga watan Maris 2024 ko Talata, 12 ga watan Maris 2024. Akwai inda za a yi azumi maintsawo.
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya yi musayar kalamai masu zafi da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas a wajen jana'izar Wigwe.
Mataimakin shugaban kasa kashim Shettima, ya yi wa 'yan Najeriya albishir da cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi musu tanade-tanade mai kyau.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci hukumar hana fasa kwauri ta kasa watau Kwastam, da ta mayar da kayan abincin da ta kwace ga mutanen da ke da su.
Gwamnatin jihar Adamawa ta shigar da kara kan dakataccen kwamishinan hukumar zabe ta INEC, Yunusa Hudu Ari, kan zargin aikata wasu laifukan zabe.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya shirya bayar da tallafi ga al'ummar jihar domin su samu sauki a lokacin gudanar da azumin watan Ramadan.
Wasu daga cikin daliban da aka sace a jihar Kaduna sun kubuta daga hannun 'yan bindigan da suka tafi da su zuwa daji. Gwamna Uba Sani ya tabbatar da hakan.
Ana zargin an yi wani cushe a majalisar dattawa a kasafin kudin shekarar nan. Akwai wani kasafin kudin da aka amince da shi da ‘yan Najeriya ba su sani ba
Manyan Labarai A Yau
Samu kari