Labaran Soyayya
Wani rahoto da muka samu ya tabbatar da cewa kotun Shari’ar Musulunci da ke Rigasa ta hana wani matashi, Salisu Salele kusantar tsohuwar budurwarsa, Bilkisu Lawal.
Rahotanni sun tabbatar da cewa kotun Majistare a Kaduna ta gurfanar da Abigail Victor mai shekara 23 bisa zargin caka wa saurayinta wuka saboda zargin yaudara.
Dakarun yan sanda sun cafke wani matashi Mansur Umar da ake zargi da halaƙa saurayin kanwarsa, Suleiman Musa a gidansu da ke jihar Kano ranar Juma'a.
'Yan sanda sun cafke wata dalibar jami'ar Ekiti bisa zargin yin garkuwa da kanta domin ta sha soyayya da saurayinta. Kwamishinan 'yan sanda ya ce za a kai ta kotu.
Matashi Mustapha PK, mai shekaru 25, ya auri Anty Samira mai shekaru 39, inda suka bayyana cewa soyayya tsantsa ce ta hada su ba kwadayi ba ko wani abu na daban.
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Goodswill Akpabio ya yi kalaman soyayya ga matarsa yayin da ya sumbace ta a idon duniya yayin da ake tsaka da rikicinsa da Natasha
Rundunar 'yan sanda ta kama wani Gbolahan Adebayo bisa zargin kashe budurwarsa da duka a Legas. An dauki gawarta zuwa asibiti domin gudanar da bincike.
Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, IBB ya bayyana yadda ya hadu da matarsa da irin tasirin da ta ke da shi a rayuwarsa da yadda ta Muslunta kawai.
Mahaifiyar fitaccen mawakin nan wanda aka fi sani da 2baba ta roki ƴar Majalisar dokokin jihar Edo, Hon. Natasha ta rabu da ɗansa domin yana cikin ruɗani.
Labaran Soyayya
Samu kari