Labarin Sojojin Najeriya
Sabon shugaban hukumar sojin kasan Najeriya, COAS Manjo Janar Taoreed Lagbaja, ya kama aiki a matsayin shugaban soji na 23 a tarihi ranar Jumu'a a birnin Abuja.
Hassan Bala Abubakar, sabon shugaban rundunar sojin saman Najeriya da shugaban ƙasa ya naɗa ya shiga Ofis bayan ya karɓi mulki daga hannu magabacinsa a Abuja.
Hedkwatar rundunar sojin ruwa ta karyata zargin da ake yi cewa shugaban rundunar mai barin gado, Awwal Gambo, ya ki mika mulki ga magajinsa, Emmanuel Ogalla.
An ji labari cewa nadin Manjo Janar Christopher Musa da su Taoreed Lagbaja zai canza shugabancin sojojin Najeriya. Sojoji da-dama za su sake ajiye khakinsu.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya tsige dukkanin shugabannin rundunar sojoji sannan ya nada Janar Taoreed Abiodun Lagbaja a matsayin sabon babban hafsan sojoji.
Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin sabbin hafsoshin soji, sufeto janar na yan sanda da kwanturola Janar na Kwastam a ranar Litinin.
An samu hafsoshin sojoji da sauran manyan jami’an tsaro. Za a ji Bola Tinubu ya kafa tarihi wajen nada guraye da wanda ya kwato $8m a matsayin Hafsoshin Tsaro
Dakarun sojin saman Najeriya sun samu nasarar sheƙe mayaƙan ƙungiyar ta'addancin ISWAP tare da kwamandojinsu a wani farmaki da suka kai maɓoyarsu a jihar Borno.
Akalla mutane goma sha biyar ne rahotanni suka kawo cewa an yi wa yankan rago a wani hari da wasu da ake kyautata zaton yan Boko Haram ne suka kai jihar Borno.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari