Labarin Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya sun ceto wasu mutane takwas da aka sace a wajen biki a jihar Kano. 'Yan bindiga sun saka kayan sojoji sun sace mutanen a karamar hukumar Shanono.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta jaddada cewa sojoji ne za su ci gaba da yanke duk wani aiki da za a iya ko da kuwa sojojin Amurka sun shigo kasar nan.
Dakarun sojojin Najeriya masu yaki da ta'addanci sun samu nasara kan 'yan ta'addan ISWAP a jihar Borno. Sojojin sun kwato makamai masu yawa a hannunsu.
A tarihin Najeriya akwai wasu manyan sojojin da aka taba yankewa hukunci kan yunkurin juyin mulki. Wasu daga cikin hukunce-hukuncen an aiwatar da su ta hanyar kisa.
Gwamnatin Amurka karkashin Donald Trump za ta turo sojoji Najeriya akalla 200 domin yaki da 'yan ta'adda a kasar. Sojojin Amurka za su horas da na Najeriya.
Hafsan tsaron Najeriya, Janar Oluyede ya sanar da cewa za a tura dakaru na musamman zuwa Kwara da Niger. Ya nemi a ƙarfafa ƴan sanda da jami'an NSCDC.
Majalisar tarayya ta yi watsi da kasafin rundunar sojin sama na 2026 saboda rashin kuɗi. An kafa kwamiti don sake fasalin kasafin da zai wadatar da ayyukan soojin.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta sha alwashin cewa duk mai hannu a harin da aka kashe daruruwan musulmi a jihar Kwara zai fuskanci hukunci daidai da abinda ya aikata.
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan jami'an tsaro a jihar Katsina. 'yan bindigan sun kai harin ne kan jami'an tsaron da ke hanyar kai daukin gaggawa.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari