Kasashen Duniya
Fadar White House ta ce Shugaban kasar Amurka, Joseph R. Biden Jr. ya zabi tawagar da za ta zo Najeriya wajen rantsar da sabon shugaban kasa da za ayi a Abuja.
Wata kyakkyawar Bahaushiya ƴar Najeriya, ta shiga cikin jerin sojojin ƙasar Amurka. Budurwar ta zama cikakkiyar sojan Amurka ne bayan sun kammala samun horo.
A jiya, Antony Blinken ya dauki kimanin minti 20 yana zantawa da zababben shugaban Najeriya. Mataimakin Kakakin Jakadancin Amurka, Matthew Miller ya fadi haka.
Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana yadda aka yi nasarar kawo karshen annobar Korona da ta addabi duniya a shekarun da suka gabata kadan da suka dame wa kowa.
An harbi jirgin kasar Turkiyya da ya je kwashe ’yan kasar da suka makale a Sudan bayan bangarorin da ke yakar juna sun amince su kara tsagaita wuta na awa 72.
Yaki ya yi kamari, Hukumomin Sudan sun nemi hana mutanen Najeriya barin kasarta. Ana cikin dar-dar a Sudan a sakamakon yakin da ya kaure tsakanin sojojin kasar.
Za a ji Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai halarci taron Kolin Shugabannin Kasashen Yankin Tekun Guinea da za a gudanar a Accra, babban birnin kasar Ghana.
Rahotanni daga babban birnin kasar Mali, sun nuna cewa harin kwantan ɓauna ya yi ajalin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa da wasu manyan mutane huɗu.
Wasu mutane sun ɗau harama sun ɗauki niyyar azumin jiran Yesu domin haɗuwa da shi. Sai dai mutuwa ta yi mu su ɗauki ɗai-ɗai a yayin da suke gudanar da azumin.
Kasashen Duniya
Samu kari