Jihar Kano
Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da shugabannin makarantun sakandare guda uku a jihar saboda rashin kula da aiki da zuwa aiki ba akan lokaci ba da wasu laifuka.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, Muhammad Gumel ya ce jami'ansu sun bazama neman makera a jihar da ke kera wukake ga masu aikata laifuka ke amfani da su.
Za a ji cewa shugabannin APC ba su yarda Abdullahi Ganduje ya canji Abdullahi Adamu a NWC ba. Har wasu da ke rike da mukamai a jam’iyya ba su boye adawarsu ba.
Tun bayan murabus na Sanata Abdullahi Adamu, jam'iyyar APC ke faman neman wanda zai maye gurbinsa, Tsohon gwamna Ganduje da Almakura na cikin masu neman kujerar
Mummunar gobara ta tashi a kasuwar Rimi da ke jihar Kano a daren ranar Laraba, 19 ga watan Yuli inda aka yi asarar dukiya. Shaguna guda 10 ne suka kone kurmus.
Kungiyar C3GR ta bukaci Shugaba Tinubu da kakakin majalisa, Abbas Tajudden da kada su ba wa Abdullahi Ganduje da Ado Doguwa mukamai saboda zargin da ke kansu.
A Kano, a auren zaurawan da gwamnatin Abba Kabir Yusuf za tayi, mata su na harin auren Sanata Kawu Sumaila, Yusuf Ogan Boye, da wani ‘Dan Majalisar tarayya.
Abba Kabir Yusuf ya nada shugabannin wasu hukumomi, cibiyoyi da kamfanonin jihar Kano. Irinsu Dr. Muhammad S. Khalil da Dr. Dahir M. Hashim aiki sun samu mukami
Tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya musanta rade-radin da ake ta yadawa na cewa gwamnatinsa ta ciyo bashin naira biliyan 10 domin sanya.
Jihar Kano
Samu kari