Jihar Kano
Rahoton nan ya tattaro wasu hukuncin shari’o’in da aka yi wanda aka yi nasara a kan Mai girma Abba Kabir Yusuf da aka fi sani da Abba Gida Gida a Kano.
Wani lauya da ke zaune a jihar Kano, Umar Sa'ad Hassan ya yi hasashen abin da zai kasance a shari'ar zaben jihar Kano, ya ce zai yi wahala Abba Kabir ya yi nasara.
Jam'iyyar NNPP mai kayan daɗi ta musanta zargin da wasu ƙungiyoyi suka yi cewa yan Kwankwasiya sun tsara mamaye kotun koli da ofisoshin jakadanci.
Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila ya yi maganar damar Abba Gida Gida a shari’ar zaben Gwamna Kano a kotun koli, Sanatan ya ce APC na harin jihar Kano ne a 2027.
Manyan jam'iyyun siyasa biyu, NNPP da APC a Kano sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya karo na uku yayin da ake dakon hukuncin kotun koli.
Gamayyar kungiyoyin Arewa a yankin kudu maso yamma sun zargi shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da hannu a rikicin siyasar da ke faruwa a jihar Kano.
Kungiyar Matasa a Arewa ta yi martani kan hukuncin shari'ar zaben jihar Kano inda ta bukaci Kotun Koli ta yi adalci da kuma bar wa mutane abin da su ka zaba.
Wani Malamin addini ya ce zalunci ne a tsige Abba Kabir Yusuf daga mulki duk da yana ganin Abba ya fara mulkinsa da kuskure wajen rushe rushen dukiyar mutane.
'Yan Arewa mazauna Kudancin Najeriya sun fito zanga-zanga kan hukuncin shari'ar zaben jihar Kano inda su ka bukaci a yi adalci cikin hukuncin da za a yanke.
Jihar Kano
Samu kari