Jihar Kano
Jigon jam'iyyar NNPP, Buba Galadima ya bayyana Janar Sani Abacha a matsayin mafi kyawun shugaban kasar Najeriya idan aka kwatanta da sauran da aka taba yi.
Gwamna Abba Kabir ya umarci kwamishinan 'yan sanda, Hussaini Gumel ya fitar da sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga fadar Nasarawa a jihar Kano.
Babbar Kotun Tarayya ta yi hukunci kan dambarwar masarautun jihar Kano tsakanin Sanusi II da Aminu Ado Bayero a yau Alhamis 20 ga watan Yunin 2024.
An fara shiga fargaba a Kano bayan da Babbar Kotun Tarayya ta yanke hukunci kan halaccin dokar da ta rusa masarautun jihar guda biyar da kuma nadin Sanusi II.
Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta yi wats da dokar da majalisar dokokin Kano ta yi amfani da ita wajen nada Muhammadu Sanusi II sarkin Kano.
Dokar majalisar masarautar Kano ta 2024, wacce ta rusa masarautun jihar guda biyar na nan daram amma kotu ta lalata matakan da gwamnan ya dauka na aiwatar da dokar.
Babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta sanar da cewa za ta ci gaba da zaman shari'ar kan rigimar sarautar Kano da misalin karfe 2:00 na rana yau Alhamis.
Rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta sanar da mutuwar wani mutum guda daya tare da jikkata jami'anta biyu yayin da ake tsaka da shari'ar sarautar Kano.
Rundunar ƴan sanda ta yi kira ga mazauna jihar Kano su zauna lafiya yayin da ake jiran hukuncin Babban Kotun Tarayya kan rigimar sarauta yau Alhamis.
Jihar Kano
Samu kari