Rikcin makiyaya a Najeriya
Wasu makiyaya dauke da makamai sun kai farmaki kan wasu kauyukan jihar Jigawa a Arewacin Najeriya. Makiyayan sun raunata mutum takwas tare da lalata gonaki.
Rikicin manoma da makiyaya a jihar Jigawa ya yi jawo asarar rayukan mutane uku a yankin gandun dajin Baranda da ke karamar hukumar Kiyawa, har an ceto wasu.
Rundunar 'yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da cewa an samu rikici tsakanin manoma da makiyaya a karamar hukumar Birnin Kudu ta jihar. Mutum biyar sun raunata.
Wani makiyayi mai suna Wuzaifa Salisu ya sare hannun wani manomi mai suna Bitrus Chawai yayin da ya afka masa a gona. Dan uwan Bitrus ne ya bayyana lamarin.
Kungiyar manoma da makiyaya sun saka hannu kan yarjejebiyar zaman lafiya a yankin kudu maso yammacin Najeriya. Ana sa ran matakin zai kawo zaman lafiya.
Wasu gungun mata sun fantsama kan tituna suna zanga-zangar nuna adawa da yawan hare-hare da kashe-kashen ƴan bindiga a yankunansu a Bokkos da Mangu.
An bayyana yadda Fulani suka zargo sojojin Najeriya da aikata masu barnar da ba za su iya daukar mataki ba a Plateau. Sun bayyana yadda aka kone gidajensu.
Rikicin da ya barke tsakanin Hausawa da Fulani a karamar hukumar Gudu, jihar Sokoto ya yi sanadin mutuwar mutane hudu, ana zargin saɓani a kan gona ne ya jawo fadan.
An samu asarar rayuka a sabon rikicin da ya barke tsakanin wasu fusatattun matasa a jihar Filato. An kona gidaje da rumbunan hatsi masu dumbin yawa.
Rikcin makiyaya a Najeriya
Samu kari