Babban kotun tarayya
Hukumar EFCC ta sake gabatar da wata hujja a gaban kotu wadda ta bayyana yadda tsohon gwamnan CBN, Emefiele ya ba kamfanin matarsa kwangilar biliyoyin Naira.
Yayin da dan takarar gwamnan Bayelsa, Timipre Sylva da jam'iyyar APC ke zargin nuna musu wariya a shari'ar zaben jihar, kotu ta yi fatali da korafin a jiya.
Wata kungiya ta shigar da kara a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja kan jam'iyyar Labour Party (LP). Kungiyar ta nemi a soke rajistar jam'iyyar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya rantsar da alkalai 9 na babbar kotun jihar Kano da kuma khadi 4 na kotun ɗaukaka ƙara ta shari'ar musulunci.
Babbar kotu da ke jihar Kano ta dauki mataki kan gwamnatin jihar da majalisa inda ta dakatar da su kan gyaran fuska a dokokin wasu hukumomi guda uku.
Bayan kammala binciken kwakwaf, Gaskiya ta bayyana kan zargin wawure dala miliyan 6.2 daga bankin CBN da aka cire da saka hannun bogi na Buhari a 2023.
Watanni biyu kacal bayan ɓaɗa shi a matsayin alkalin babbar kotun jihar Nasarawa, Mai shari'a Benjamin Makama, ya rasu bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah da ake tsare da shi, Bello Bodejo, ya shigar da gwamnati kara a gaban kotu yana neman a sake shi ba tare da wani sharadi ba.
Babbar kotun tarayya mai zama a birnin Kano ta yanke hukuncin cewa hukumar yaƙi da rashawa ta jihar Kano ba ta da ikon binciken tsohon Gwamna Ganduje.
Babban kotun tarayya
Samu kari