Nade-naden gwamnati
Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya yi magana kan sauran Ministoci da aka sallama inda ya yabawa Bola Tinubu kan daukar matakin da ya yi a gwamnatinsa.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura wasika ga majalisar dattawa domin tantance ministocin da ya zaɓo. A ranar Laraba majalisar dattawa za ta tantance ministocin.
Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa Bola Tinubu ya yi la'akari da ra'ayoyin ƴan Najeriya wajen yanke ministocin za a kora, ta faɗi tsarin da aka bi wajen tantancewa.
Mutanen yankin Neja Delta sun caccaki Bola Tinubu kan zargin rusa musu ma'aikata. Wasu daga cikinsu sun yi madalla da rusa ma'aikatar da Bola Tinubu ya yi.
Sabon shugaban hukumar da'ar ma'aikata (CCB), Abdullahi Bello ya sha alwashin raba ma'aikatan kasar nan da cin hanci da rashawa tare da dawo da martabar aiki.
Tsohuwar Ministar harkokin mata, Uju Kennedy Ohanenye ta yi magana awanni kadan bayan sallamar ta daga mukaminta inda ta yi godiya ga Shugaba Bola Tinubu.
Jam'iyyun adawa sun ce korar ministoci da Bola Tinubu ya yi a banza ne, PDP ta ce korar ministoci kora kunya ne. LP ta ce Tinubu ya fara korar yunwa kafin ministoci.
Gwamnan jihar Benue, Alia Hyacinth ya dakatar da kwamishinan shari'a kan shiga shari'ar kalubalantar dokar da ta kirkiri EFCC ba tare da saninsa ba.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya godewa mutum 5 da ya sallama daga matsayin ministoci tare da yi masu fatan alheri a duk harkokin da za su sa a gaba.
Nade-naden gwamnati
Samu kari