Nade-naden gwamnati
Akwai yiwuwar shugaban kasa, Bola Tinubu ya nada tsohon shugaban masu tsaron marigayi Sani Abacha, Mejo Hamza Al-Mustapha mai ritaya a matsayin kwamandan NSCDC.
Shugaba Bola Tinubu ya nada sabon shugaban Hukumar ICPC, Dakta Adamu Aliyu wanda zai jagoranci hukumar wurin ci gaba da yaki da cin hanci a Najeirya.
An rahoto cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada Fatima Faruk a matsayin babbar mai ba shi shawara kan harkokin mata. An sanar da hakan ne a ranar Litinin.
Gwamnan Kaduna ya zabi Dr. Abdulkadir Mayere a matsayin sabon Sakataren Gwamnati. Uba Sani ya fitar da sanarwa ta musamman ta ofishin Sakatarensa na yada labarai.
Shugaba Bola Tinubu ya nada 'yar takarar sanata a jam'iyyar APC a mazabar Abuja, Adedayo Benjamins-Laniyi a matsayin sakatariyar mata a hukumar FCTA.
Rashin gane inda aka dosa ya haifar da rigimar da ma'aikata su ke yi a Hukumar NIPOST. Ma’aikata sun barke da zanga-zanga saboda nadin da Shugaban kasa ya yi.
Babban lauya a Najeriya, Femi Falana ya soki Bola Tinubu kan nadin shugabannin EFCC da ICPC dukkansu a yankin Kudu maso Yammacin kasar, ya ce ya sabawa doka.
Gwamnatin tarayya ta sake nada Sunday Adepoju awanni bawan an kore shi daga kujerarsa. Shugaban NIPOST din ya koma ofis, yana cewa Bola Tinubu ya maida sa.
Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za ta fara aiki gadan-gadan a makon nan. Shugaba Bola Tinubu zai gana da Ministocinsa bayan makonni da rantsar da FEC
Nade-naden gwamnati
Samu kari