Nade-naden gwamnati
Kwanaki kadan bayan mutuwar Walin Zazzau, Sarki Ahmed Nuhu Bamalli ya nada ɗansa, Abdullahi Nuhu Bamalli a matsayin sabon Walin Zazzau a jihar Kaduna.
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu masana’antar kera motoci ta Najeriya ta shirya ta fara aiki gadan-gadan, kuma za a fara fitar da ababen hawan daga watan Disamba.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi sabbin nade-nade a manyan hukumomi biyu a Najeriya da suka hada da hukumar SEC da Kuma NAICOM a yau Juma'a.
A ranar Laraba, 15 ga Afrilu, gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya amince da nadin Alhaji Falalu Bawale a matsayin shugaban ma'aikatana jihar.
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya yi kakkausar suka kan kungiyar Dattawan Arewa inda ya kalubanci masu mukamai a yankin su kare gwamnatin Bola Tinubu.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada sabon manajan daraktan kamfanin FHAEDL. Injiniya Kabir Musa Umar shi ne aka nada a wannan mukamin a kamfanin.
Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ya naɗa tare da tura sunayen sababbin kwamishinoni zuwa ga majalisa dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su.
Babbar kotun jiha ta soke naɗin Olola na Ola, Oba Johnson Ajiboye, wanda Gwamna Ademola Adeleke ya yi saboda abin da ta bayyana da rashin bin tsarin doka.
A cewar wata majiya ta kusa da marigayin, Ogbonnaya Onu wanda tsohon ministan kimiyya da fasaha a mulkin Buhari, ya rasu a Abuja bayan fama da rashin lafiya.
Nade-naden gwamnati
Samu kari