Yan bindiga
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki kan wasu manoma dake tsaka da gudanar da aiki a gonakinsu a jihar Katsina. Sun hallaka mutum uku har lahira.
Gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu ya ce gwamnatinsa na daukar sababbin matakai domin yakar rashin tsaro a fadin jihar baki daya duba da ƙaruwar matsalar.
Wata kungiyar Arewa maso Yamma ta nemi gwamnan Zamfara ya yi murabus saboda gazawarsa a tsaro da ilimi, tana mai cewa Zamfarawa sun cancanci fiye da haka.
Sheikh Musa Assadus Sunnah ya yi magana a bidiyo inda ya ƙaryata rahoton kama yan uwan Ado Aliero a Saudiyya inda ya ce babu wata hujja da ke nuna suna da alaƙa.
Daya daga cikin lauyoyin Hamdiyya Sidi Shareef da ake kira Abba Hikima ya tabbatar da batan matashiyar a birnin Sokoto wanda ake nemanta tun jiya bayan fita sayayya.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai sake kai harin ta'addanci a jihar Kogi. Miyagun sun yi awon gaba da wasu mutanen da ba su hawa ba, ba su san sauka ba.
Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma a majalisar dattawa, Sunday Karimi, ya danganta dawowar matsalar rashin tsaro a kan yunkurin bata gwamnatin Bola Tinubu.
Mutane a wasu yankuna na jihar Zamfara musamman karamar hukumar Kaura na Moda na barin gidajensu da dare su dare da safe saboda tsaron hare hare.
Bayan matasa sun gudanar da zanga-zanga kan zargin basarake da ta'addanci, Sarkin Daura, Alhaji Faruq Faruq ya sauke dagacin kauyen a Katsina, Iliya Mantau.
Yan bindiga
Samu kari