Yan bindiga
A ranar Jumu'ah da ta gabata yan bindiga sama da 300 suka kai hari garin Kuchi da ke jihar Neja suka kama mutane da dama. Yan bindigar sun zauna a garin.
Jami'an tsaro na 'yan sanda sun yi nasarar hallaka wasu mutum biyu da ake zargin masu garkuwa da mutanen ne a jihar Kogi. Sun kuma kwato makamai.
Ƴan bindiga sun gindaya sharuda ga wasu manoma a yankin Unguwar Jibo da Nasarawa da ke karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna kan laifuffukan da suka aikata.
Rundunar ‘yan sandan Katsina ta musanta labarin cewa 'yan ta'addan da suka kai hari jihar sun kashe mutane 40 kamar yadda aka yayatawa a wasu wuraren.
Rundunar 'yan sanda a jihar Kogi da ke Arewacin Najeriya ta sanar da cewa ƴan bindiga sun yi ajalin daliban Jami'ar jihar da suka sace a farkon wannan wata.
Mambobin majalisar dokokin jihar Benuwai guda shida sun tsallake rijiya da baya yayin da wasu ƴan bindiga suka kai hari kan titin Makurdi zuwa Gboko.
Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Kaduna sun samu nasarar cafke wani kasurgumin dan bindiga a jihar. Jami'an tsaron sun kuma ceto mutum uku da aka sace.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ta dade tana addabar kasar nan. Ya bukaci gwamnati ta tashi tsaye.
Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta yi martani kan zargin da gwamnan jihar Katsina ya yi na cewa jami'an tsaro na hada baki da 'yan bindiga. Ta bukaci ya kawo hujja.
Yan bindiga
Samu kari