Yan bindiga
Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan bindiga sun sace Blessing Adagba, mai taimakawa Gwamnan Ebonyi, a unguwar Okposhi Eheku da ke karamar hukumar Ohaukwu.
Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan bindiga sun kai farmaki a Rijiya da ke Zamfara, inda suka kashe mutane takwas tare da kona wata makarantar firamare.
Janar Maharazu Tsiga ya bayyana irin wahalar da ya sha a hannun 'yan bindiga bayan shafe wata biyu a tsare a daji inda ya fadi yadda suke kwana da dabbobi.
An miƙa Janar Tsiga da mutane 18 da aka ceto ga Nuhu Ribadu bayan ya shafe kwanaki 56 a hannun ‘yan bindiga. Ribadu ya yabawa jami’an tsaro kan wannan nasarar.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-hare a kauyukan karamar hukumar Safana. Sun hallaka kwamandan 'yan sa-kai tare da wasu mutane.
Bayan kwanaki 56 a hannun masu garkuwa, Janar Tsiga ya samu 'yanci. Iyalansa sun biya kuɗin fansa, amma an ci gaba da tsare shi na tsawon sati guda.
Wasu shugabannin 'yan bindiga a jihar Zamfara sun haukace bayan shan miyagun kwayoyi. Wasu na ganin zafafan addu'o'i da ake musu ne yasa suka haukace.
‘Yan bindiga sun kashe mutane 10 a Ruwi, Bokkos. Rundunar ‘yan sanda ta tura jami’ai, yayin da gwamnatin Filato ke kokarin kawo karshen hare-haren.
Rahotanni suka ce ana zargin kashe Isuhu Yellow wata alama ce ta rikicin da ke tsakanin Aleru da Gide, wanda ke haddasa tashin hankali da asarar rayuka a Zamfara.
Yan bindiga
Samu kari