Jihar Ekiti
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC ta fara kidaya da sanar da sakamakon kuri'un da al'umma suka kada a zaben gwamnan jihar Ekiti yau Asabar.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta, INEC ta ayyana gwamna mai ci, Biodun Oyebanji na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Ekiti na 2026.
Jam’iyyar APC mai mulki ta doke ɗan takarar ADC, Ambasada Dare Bejide, a rumfarsa ta zaɓe da ke Ilawe-Ekiti, inda APC ta samu ƙuri’u 140, ADC kuma 37.
Bayan samun jinkiri na yan sa'o'i, hukumar INEC ta fara dora sakamakon zaben gwamnan jihar Ekiti a shafinta na tattara sakamako watau IReV da yammacin Asabar.
Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya yi Allah-wadai da kona ofishin ‘yan sanda a Isan-Ekiti, yana mai cewa lamarin ba shi da alaƙa da zaɓe.
Rahotanni sun nuna cewa an raunata dan ADC da rigima ta kaure tsakanin magoya bayan jam'iyyun APC da ADC kan sayen kuri'u a zaben gwamnan jihar Ekiti.
‘Yan sandan Najeriya sun gargadi masu aikata laifuffukan zabe a Ekiti, yayin da suka sanar da kammala shirin samar da tsaro yayin zaben gwamnan jihar.
Hukumar zabe ta kasa ta kammala shirin gudanar da zabe a Ekiti, Kano, Nasarawa, Ondo, Enugu da Rivers a yau Asabar. Jami'an tsaro sun shirya tsaf.
Jam'iyyar PDP ba ta da jiha ko daya a yayin da ake shirin zaben gwamnan jihar Ekiti na 2026, APC mai mulki ce a sahun gaba da jihohi sama da 30 a Najeriya.
Jihar Ekiti
Samu kari