Jihar Ekiti
Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun damƙe mutane 13 da ake zargi suna da hannu a kisan da aka yi wa sarakuna 2 ranar Litinin a jihar Ekiti.
Ministan harkokin ci gaban ma'adanai, Dele Alake ya nesanta kansa da dukkan fastocin yakin neman zaben da ke yawo a soshiyal midiya cewa zai nemi takara a Ekiti.
A ranar Talata, 30 ga watan Janairu, Sanata Shehu Sani ya ce ya zama dole a hukunta wadanda suka kashe sarakunan Ekiti biyu. Ya yi addu’ar Allah ya ji kansu.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna alhihinsa kan kisan da aka yi wa wasu sarakunan gargajiya a Ekiti, ya kuma umarci ceto daliban da aka sace a jihar.
Wani dan majalisar wakilai ya kasa danne zuciyarsa kan matsalar tsaron da ake fama da ita a jihar Ekiti. Dan majalisar ya fashe da kuka yayin da ya nemi a kai dauki.
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi awon gaba da wasu yara ‘yan makaranta da ba a tantance adadinsu ba a karamar hukumar Emure da ke jihar Ekiti.
An shiga tashin hankali bayan 'yan bindiga sun yi ajalin wasu manyan sarakunan gargajiya a karamar hukumar Ikole da ke jihar Ekiti a Kudancin Najeriya.
Masu garkuwa da mutane sun sace wasu mutane da ba a san adadinsu ba a hanyar titin Akure/Ikere. Jami'ar Yan sanda Funmi Odunlami ta tabbatar da lamarin.
A wani abu kamar almara, wasu 'yan daba sun farmaki asibitin Ekiti kuma sun yi awon gaba da wata gawa. Lamarin ya faru a ranar Litinin, inda suka lalata kayayyaki.
Jihar Ekiti
Samu kari