Abuja
A yau Litinin ne ake sa ran Atiku Abubakar zai shiga jam’iyyar ADC a mazabarsa ta Jada da ke Adamawa, bayan jinkiri na watanni. ADC ta bayyana dalilin jinkirin.
Shugaba Bola Tinubu ya umarci a janye dukkan ‘yan sanda da ke rakiyar manyan kasa nan take, a mayar da su kan aikin tsaro a yankunan da ke fama da karancin jami’ai.
Jam'iyyar PDP ta soki rufe makarantu da gwamnati ta yi saboda sace-sacen dalibai, ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya nemi taimako ko ya yi murabus idan ba zai iya ba.
Yara sun fara barin FGGC Bwari bayan umarnin gwamnati na rufe makarantu 47 saboda barazanar tsaro da yawaitar sace dalibai a Arewa. Iyaye sun yi martani kan hakan.
Babbar kotun tarayya Abuja ta karyata labarin cewa an yi yunkurin kashe Justice James Omotosho bayan hukuncin da ya yanke wa Nnamdi Kanu, tana kira da a yi bincike.
Kotun Tarayya ta karyata labarin cewa an yi yunkurin hallaka Mai Shari'a, James Omotosho saboda hukuncin da ya yanke kan Nnamdi Kanu a makon jiya.
Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya ce gwamnati ba ta gurfanar da masu zargin daukar nauyin ta’addanci ba saboda binciken lamuran yana da sarkakiya.
Hukumar DSS ta gurfanar da mutum 2 a Abuja kan zargin ta’addanci da kiran juyin mulki, ciki har da wanda ake zargi da harin Okene; an dage shari'ar zuwa 2026.
Hukumar DSS ta tura Nnamdi Kanu zuwa gidan gyaran hali na Sokoto bayan kotun tarayya ta Abuja ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai bisa laifin ta’addanci.
Abuja
Samu kari