Majalisar dokokin tarayya
Majalisar dattawan kasar nan ta bayyana cewa ma'aikatu da hukumomin gwamnati za su fara bayyana don kare kasafin kudinsu a gabanta kafin aincewa da shi.
Wike ya shirya karbar makudan kudi daga mamallaka filaye a Abuja. Za a tatso biliyoyin Naira daga masu matsala da takardar mallakar kadara a Maitama.
Sanata Ali Ndume ya ji dadin sakamakon adawa da kudirin haraji domin inganta rayuwar jama'a. Ya bayyana cewa an fara samun sakamakon da ake bukata.
Shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Tajudden Abbas ya ƙaryata labarin da ake yaɗawa game da kwace masa fili a Abuja inda ya ce ko sisin kwabo ba a binsa.
Bayan kwace filayen Muhammadu Buhari da yan siyasa, Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ba da wa'adin mako biyu ga wadanda abin ya shafa da su biya kudin da ake bukata.
Tsohon shugaban majalisa, Yakubu Dogara ne ya bayyana haka. Ya shawarci 'yan Arewa jagororinsu ne su ka gaza a shekaru 40 da aka shafe ana mulkin kasar.
Yar majalisar wakilan tarayya kuma ɗiyar tsohon gwamnan jihar Delta, Ibori-Suenu ta ce kwanan PDP ya kare a mazaɓarta, za ta jagoranci birne ta a kogi.
Dan majalisar Kaduna ya ce kudin jama'a na zurarewa ta ko'ina, ta hanyar kasadin kudin shekara-shekara. Ya ce bai dace a rika barnar kudin 'yan Najeriya ba.
Shugaban kwamitin kudirin haraji Taiwo Oyedele ya ce 'yan Najeriya suna zaginsa a kafafen sada zumunta a kan aikin da ya dauko na kawo gyara a kasar nan.
Majalisar dokokin tarayya
Samu kari