An Nemi Tinubu Ya Sauke Shettima Ya Dauko Gwamnan Bauchi a 2027

An Nemi Tinubu Ya Sauke Shettima Ya Dauko Gwamnan Bauchi a 2027

  • 'Yan siyasa a kasar nan na cigaba da yi wa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kira daban-daban game da zaben 2027 da ke kara karatowa
  • Wata kungiya a jihar Bauchi ta yi kira ga shugaba Tinubu ya ajiye mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima ya dauki gwamna Bala Mohammed
  • A bayanin da ta yi, kungiyar ta yi alkawarin yin gangami na musamman domin tara miliyoyin mutane da za su marawa Bola Tinubu baya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Wata kungiya ta magoya bayan gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, ta roki Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya zabi gwamnan a matsayin abokin takararsa a zaben 2027.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake rade-radin cewa Sanata Bala Mohammed zai iya komawa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Kara karanta wannan

Amurka ta gabatar da 'tayi na karshe kuma mafi kyau' ga tawagar Iran a teburin tattaunawa

Kashim Shettima, Bala Mohammed da Bola Tinubu
Kashim Shettima a hagu, Bala Mohammed a tsakiya da Bola Tinubu a dama. Hoto: Kashim Shettima|Lawal Muazu Bauchi|Bayo Onanuga
Source: Facebook

Leadership ta wallafa cewa kungiyar mai suna Kaura Diehard Supporters a Jihar Bauchi, ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da shugabanta, Mustafa Abdullahi Duguri, ya fitar.

Kokarin Gwamna Bala Mohammed a Bauchi

Duguri ya bayyana Bala Mohammed a matsayin shugaba mai kawo sauyi, mai kwarewar siyasa da kuma kyakkyawan tarihin aiwatar da ayyukan more rayuwa, yana mai cewa ya dace da mukamin mataimakin shugaban kasa.

A cewar kungiyar, gwamnan ya samar da gagarumin ci gaba a Jihar Bauchi ta hanyar manufofi masu amfani da kyakkyawan shugabanci, wanda ya sa ake ganin shi daya daga cikin fitattun shugabanni a yankin Arewa maso Gabas.

Ta kuma ce yunkurinsa na hada kai da jam’iyya mai mulki duk da kalubale siyasa ya nuna ya kamata a saka masa da mukamin mataimakin shugaban kasa.

“Gwamna Bala ya kafa kansa a matsayin shugaba mai aiki a yankin Arewa maso Gabas. Muna da yakinin cewa yana da karfin kawo kuri’un yankin ga shugaban kasa a 2027,”

Kara karanta wannan

2027: Maituta ya kara farin jini a wurin jama'a, ana so ya fito ya 'ceci' jihar Zamfara

In ji shugaban kungiyar.

Kungiyar ta kuma jaddada nasarorin da ya samu a fannin gine-gine da abubuwan more rayuwa, tana mai cewa hakan zai ba shi damar daukar nauyin manyan mukamai a matakin kasa.

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed
Gwamna Bala Mohammed yayin wani taron nadin sarauta a Bauchi. Hoto: Lawal Muazu Bauchi
Source: Twitter

Alkawarin kungiyar ga Tinubu

Kungiyar ta kara da cewa mambobinta a shirye suke su hada taron goyon baya daga tushe, ciki har da shirya gangamin mutane miliyan 10 domin goyon bayan tikitin Tinubu/Bala a zaben 2027.

Fadar shugaban kasa bata fito ta yi magana kan bukatar kungiyar ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton, duk da ana rade-radin Sanata Bala Mohammed zai sauya sheka a kwanan nan.

Sai dai Vanguard ta rahoto cewa a shekarar 2025, gwamna Bala Mohammed ya karyata cewa yana neman mukamin mataimakin shugaban kasa.

Tinubu ya magantu kan tsadar mai

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi martani kan korafin da 'yan Najeriya ke yi game da tsadar man fetur da gas.

Kara karanta wannan

Kujerar mataimakin Abba Kabir na neman jawo rigima, an roki Tinubu kan Sule Garo

Yayin wani jawabi a jihar Bayelsa, shugaban kasar ya bayyana cewa duk da farashi ya tashi a Najeriya, ana samun sauki idan aka kwatanta da Kenya da wasu kasashe.

Martanin Bola Tinubu ya zo ne a lokacin da farashin makamashi ya tashi a duniya bayan barkewar yakin Amurka/Isra'ila da Iran a Gabas ta Tsakiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng