Kano: Yadda Aka Raba Mukaman ADC tsakanin Kwankwaso, Gawuna da Bangaren Atiku

Kano: Yadda Aka Raba Mukaman ADC tsakanin Kwankwaso, Gawuna da Bangaren Atiku

  • Ƙungiyar Kwankwasiyya ƙarƙashin jagorancin Rabiu Musa Kwankwaso ta amince da wani kaso da aka ware na mukaman shugabanci a ADC a Kano
  • Yarjejeniyar ta haɗa da ɓangarorin Atiku Abubakar da Nasiru Gawuna, inda aka raba mukamai domin haɗa kai da ƙarfafa jam’iyyar
  • An bayyana cewa tsarin rabon mukaman zai taimaka wajen samar da shugabanni daga matakin ƙaramar hukuma zuwa jiha cikin adalci da haɗin kai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Ƙungiyar Kwankwasiyya a cikin jam’iyyar ADC ta amince da karɓar kashi 30 cikin ɗari na mukaman shugabanci a Kano.

Hakan ya biyo bayan tattaunawa mai zurfi tsakanin ɓangarori daban-daban da ke a jihar Kano.

ADC ta tsara rabon shugabanci tsakanin Kwankwaso, Atiku da Gawuna saboda gudun rikici
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar, Rabi'u Musa Kwankwaso.
Source: Twitter

Ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ta cimma yarjejeniya da ɓangaren Atiku Abubakar da kuma na Nasiru Yusuf Gawuna, cewar The Guardian.

Kara karanta wannan

Kashe kashe a Najeriya ya damu Atiku sosai, ya yaba wa gwamnatin Amurka

Yadda aka tsara mukaman ADC a Kano

Dukkanin Kwankwaso da Gawuna sun fice daga jam’iyyunsu na baya, inda suka koma ADC domin sake tsara siyasar su da ƙoƙarin karɓe iko daga jam’iyya mai mulki a Kano.

Kwankwaso ya sake duba dabarunsa na siyasa domin ci gaba da riƙe tasirinsa a Kano, bayan ya rasa ikon tsarin da ya samar da gwamna Abba Kabir Yusuf.

A ƙarshe, ɓangaren Atiku Abubakar ya samu kashi 40 cikin ɗari na mukaman shugabanci, yayin da na Gawuna da Kwankwasiyya suka samu kashi 30 cikin ɗari kowanne.

ADC ta raba fada tsakanin Kwankwaso, Atiku ga Gawuna
Jagoran siyasar Kwankwasiyya, Rabi'u Kwankwaso. Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Martanin jam'iyyar ADC a Kano

Mai magana da yawun jam’iyyar na riƙo, Sa’id Bello, ya ce wannan tsari zai taimaka wajen haɗa kan dukkan ɓangarorin jam’iyyar a Kano.

Bello ya bayyana cewa tsarin rabon mukaman zai shafi matakai daga ƙananan hukumomi har zuwa jiha, domin tabbatar da adalci da wakilci ga kowa.

Ya ƙara da cewa:

“Ƙungiyar Kwankwasiyya za ta riƙe kashi 30 cikin ɗari, yayin da tsohon tsarin ADC na hannun mabiyan Atiku zai riƙe kashi 40 cikin ɗari”.

Kara karanta wannan

Iran ta dauki wani mataki da ya sa ta shiga gaban Amurka a shirin zaman sulhu a Pakistan

Ya kuma ce ɓangaren da ke biyayya ga Nasiru Yusuf Gawuna zai samu kashi 30 cikin ɗari na mukaman shugabanci a jam’iyyar, cewar Tribune.

Taron ya samu halartar manyan jiga-jigan siyasa ciki har da Kwankwaso, Aminu Abdussalam, Akilu Indabawa, Nasiru Gawuna, da Sanata Rufa’i Sani Hanga.

Sanata Lawal Adamu Usman ne ya jagoranci taron, inda aka ba shi alhakin tabbatar da haɗin kai tsakanin ɓangarorin jam’iyyar ADC a Kano.

An gudanar da taron a gidan Kwankwaso a Kano, inda aka tattauna hanyoyin da za su tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaɓe mai zuwa.

Fasto ya yi hasashen sabon shugaban kasa

Mun ba ku labarin cewa wani malamin addinin Kirista a Najeriya ya yi hasashe game da zaben shugaban kasa na shekarar 2027 da ake tunkara.

Fasto Solomon Emeka Eliyah ya yi hasashen da ya ba mutane mamaki saboda ya nuna shugaba Bola Tinubu bai da nasara a zaben.

Malamin ya gargadi cewa duk wani yunkurin magudin zabe zai iya haifar da abubuwan da ba a taba gani ba a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.