APC: Tsohon Saƙon Shugaban INEC Ya Jawo Zazzafar Muhawara kan Sahihancin Zaben 2027
- Tsohon sakon X da ake dangantawa da shugaban INEC, Joash Amupitan ya tayar da sabon rikici a kan babban zaɓe mai zuwa
- Duk da yunƙurin da fitaccen mai sharhi, Farouk Kperogi ya yi n binciko saƙon, hukumar INEC ta ce ƙarya ake yi wa Amupitan
- ‘Yan Najeriya sun rabu kan sahihancin zargin da tasirinsa ga amincewa da zaɓe zuwa ganin alaƙar da ake zargin hana da ita da APC
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja –Wani sabon rikici ya barke kan zargin tsofaffin sakonnin kafafen sada zumunta da ake alakanta su da shugaban hukumar zabe ta ƙasa INEC, Farfesa Joash Amupitan.
Rahoton ya ce ana zargin ya taba yin kalaman goyon bayan jam’iyyar APC a lokacin zaben 2023, wanda ke nufin yana da ra'ayin jamiyya.

Kara karanta wannan
Tsohon ɗan majalisa ya ƙare kansa kan zargin fitar da bayan sirrin Najeriya ga ƙasashen waje

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa sai dai INEC ta fito ta musanta wannan zargi, tana mai cewa shugaban hukumar ba shi da wani asusu a dandalin X.
Batun shugaban INEC ya jawo magana
Lamarin ya kara daukar hankali ne bayan wani masani dan Najeriya mazaunin Amurka, Farooq Kperogi, ya wallafa wani rubutu a shafinsa na Facebook inda ya yi zargin cewa tsofaffin sakonni ne daga wani asusu mai dauke da sunan Amupitan.
Kalaman da aka rubuta sun nuna goyon baya ga jam'iyyar APC, daga ciki har da kalaman da ake ganin suna mara wa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu baya.
A daya daga cikin sakonnin da ake magana a kai, an rubuta:
"Nasara ta tabbata."
Ana zargin ya rubuta waɗannan malamai ne yayin mayar da martani ga sakon Dayo Israel, jagoran matasan APC na kasa a wancan lokacin.
Ƴan Najeriya na shakku kan shugaban INEC

Kara karanta wannan
DSS ta gano tsohon 'dan majalisa da ya kada hantar Amurka da rashin tsaro a Najeriya
Ƴaan Najeriya da dama sun fara tofa albarkacin bakinsu a shafukan sada zumunta, inda aka samu ra’ayoyi mabambanta kan sahihancin zargin da kuma tasirinsa ga gaskiya da adalcin zabe.
Wasu sun bayyana cewa idan aka tabbatar da zargin, hakan na iya kawo babbar matsala ga shugaban hukumar zabe.

Source: Facebook
Wata mai amfani da X, Gloria O, ta ce:
"Hujjoji sun nuna ya karkata ga APC sosai, kuma ba daidai ba ne a musanta hakan.
Wani kuma, Sheidu Tijani, ya ce:
"Ya za a kama mai irin wannan muhimmin mukami dumu-dumu sannan ya rika musawa?" Onyekachi Akoma ya ce:
"Ka hakura, ka sauka daga mukamin."
Sai dai a martaninta, hukumar INEC ta kasa ta bayar da tabbacin cewa Amupitan ba shi da wani asusun a dandalin X, tare da bayar da tabbacin cewa za a yi zabe mai cike da adalci ga ƴan Najeriya.
Shugaban INEC ya hango barazana ga zaben 2027
A baya, mun wallafa cewa kallo ya fa komawa kan babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara nan da wasu watanni masu zuwa a dukkanin jihohi da ke Najeriya.

Kara karanta wannan
Wahalar da na sha a APC ko shugaban jam'iyya bai sha ba in ji Diyar Buba Galadima
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa akwai abin da yake barazana ga babban zaben 2027 da ke tafe.
Farfesa Amupitan ya bayyana cewa akwai rawar da kafafen yada labarai za su taka wajen ciyar da dimokuradiyyar Najeriya gaba, musamman ta fuskar tasa bayanan kwarai.
Asali: Legit.ng