Tsohon Ɗan Takarar Gwamna Ya Ragewa NNPP Ƙarfi a Katsina gabanin 2027
- Tsohon dan takarar gwamna na NNPP a Katsina, Injiniya Mohammed Nur Khalil, ya ajiye fice daga jam’iyya
- Nur Khalil ya ce ya dauki matakin ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma yin nazari mai zurfi
- Tsohon ɗan takarar gwamnan ya ayyana matakin da zai dauka yayin da gangar siyasar 2027 ke kara zaƙi
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina– Tsohon dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP a jihar Katsina, Injiniya Mohammed Nur Khalil, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar a hukumance.
Nur Khalil, wanda ya kasance dan takarar gwamna na jam’iyyar a zaben 2023 kuma daya daga cikin fitattun shugabannin da ke fada a ji a jihar.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa amma tsohon ɗan takarar ya bayyana rabuwa da NNPP a cikin wata wasika da ya rubuta ranar 10 ga Afrilu, 2026.
Tsohon ɗan takarar gwamna ya bar NNPP
Thisday ta wallafa cewa Nur Khalil ya aike da wasikar murabus dinsa ne ga shugaban jam’iyyar na jihar ta hannun shugabannin mazabarsa a Kandarawa.
A cikin wasikar, ya bayyana cewa ya yi wa jam'iyyar aiki tukuru domin jagorantarta a wani muhimmin lokaci na zaben da ya gabata.
Ya bayyana cewa ya ji dadin damar da ya samu na jagorantar jam’iyyar a lokacin da ake matukar bukatar hakan.
Khalil ya kuma yi alfahari da manufofin da ya jagoranta, inda ya ce sun mayar da hankali ne kan bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al’umma a jihar Katsina, tare da inganta jin dadin rayuwar jama’a.
Tsohon ɗan NNPP zai sauya sheka
Dangane da dalilin ficewar tasa, Nur Khalil ya ce matakin ya biyo bayan lokaci da ya dauka na yin nazari mai zurfi da kuma tuntuba da abokan siyasa da masu ruwa da tsaki.
Ya bayyana wannan lokaci da cewa:
"Wani lokaci ne na zurfin tunani da kuma tattaunawa mai fadi wanda ya nuna yiwuwar sauyin alkiblar siyasar sa."

Source: Original
Sai dai duk da wannan mataki da ya dauka, But Khalil bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba bayan ficewarsa daga NNPP.
Ana sa ran cewa a nan gaba kadan zai bayyana matsayirsa a fili, tare da bayyana sabuwar jam’iyyar da zai shiga ko kuma matakin da zai dauka a siyasa.
Duk da haka, wannan mataki nasa ya kara nuna yadda siyasar jihar Katsina ke ci gaba da sauyawa a hankali kamar sauran jihohi Najeriya gabanin 2027.
Ƴan NNPP sun sauya sheka
A baya, mun wallafa cewa wasu yan jam’iyyar NNPP sama da 1,000 sun sauya sheƙa daga jam'iyyar NNPP a Kano saboda wasu dalilai guda uku zuwa APC.
Wadanda suka saura shekan sun yaba da ayyukan da Shugaba Bola Tinubu ke bazawa a Najeriya da jihar Kano, tare da bayyana cewa abin da ya ja hankalinsu ke nan.
Sun kuma sanar da cewa daga yanzu sun karbi shahadar APC ta hannun mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin domin hidimta wa jam'iyyar.
Asali: Legit.ng

