2027: Maituta Ya Kara Farin Jini Wurin Jama'a, Ana So Ya Fito Ya Ceci Jihar Zamfara
- Farin jinin Sanusi Turaki Maituta na kara karuwa a siyasar jihar Zamfara yayin da zaben 2027 ke karan kusantowa a Najeriya
- Matasa, masana da masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa siyasar jihar Zamfara na iya canza wa matukar Maituta ya ayyana fitowa takara a 2027
- Ana ganin cewa zai iya kawo sauyi tare da ceto jihar daga matsalolin da ta tsinci kanta a ciki musamman batun tsaro
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - Tasirin siyasar Sanusi Turaki Bala Maituta na kara karfi a Zamfara, inda manyan ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki ke sake nazari tare da rokon ya dawo ya nemi takara a 2027.
Wannan ci gaba na zuwa ne a daidai lokacin da siyasar jihar ke fuskantar sauye-sauye masu girma, ciki har da sauya shekar Gwamna Dauda Lawal daga PDP zuwa APC mai mulki.

Kara karanta wannan
DSS ta gano tsohon 'dan majalisa da ya kada hantar Amurka da rashin tsaro a Najeriya

Source: Facebook
Farin jinin Maituta na karuwa a Zamfara
A wani rahoton da The Guardian ta fitar, masu lura da al’amuran siyasa sun bayyana cewa komawar Maituta cikin harkokin siyasa na iya kawo sauyi mai girma a Zamfara.
Ana ganin 'dan siyasar na iya kawo sauyin da ba a yi tsammani ba musamman a cikin jam’iyyar APC, inda a baya ya taba tsayawa takarar gwamnan Zamfara a zaben 2023
Majiyoyi sun ce dawowar Maituta ta fara jan hankalin matasa 'yan siyasa, inda da dama ke kallonsa a matsayin wata sabuwar dama da za ta iya sauya akalar siyasar Zamfara.
Mutane sun kosa Maituta ya fito takara
Abokansa da magoya bayansa sun kara matsa lamba a kansa da ya fito fili ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Zamfara don kalubalantar gwamna mai ci a 2027.
Sun bukace shi da ya shiga takara domin “ceto Zamfara”, suna mai nuni da gogewarsa da kuma kwarewarsa wajen kawo ci gaba da bunkasa jihar.
Baya ga siyasa, Maituta ya shahara a harkokin kasuwanci inda yake da jarin da ya shafi fannoni daban-daban, wanda yana taimakon al'umma da su.
Haka kuma, ayyukan jin kai da yake yi sun kara masa karbuwa a tsakanin jama’a, musamman a matakin kasa, inda mutane ke jin amfanin tallafin da yake bayarwa.

Source: Original
Masana sun fara sharhi kan siyasar Maituta
Yayin da ake ci gaba da tunkarar 2027, masana na ganin matakin da Maituta zai dauka na gaba, musamman bangaren jam’iyyar da zai shiga da kawancen da zai kulla na iya taka muhimmiyar rawa wajen tantance makomar zaben gwamnan Zamfara.
Wannan na nuni da cewa siyasar Zamfara na shirin shiga wani sabon salo yayin da ake tunkarar zabe mai zuwa.
Sanata Marafa ya fice daga APC zuwa ADC
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon sanata kuma tsohon jagoran yakin neman zaben Tinubu/Shettima a jihar Zamfara, Kabiru Marafa, ya fice daga APC.
Jigon kuma babban 'dan siyasa a Najeriya ya sanar da sauya sheka zuwa jam'iyyar hadakar 'yan adawa ta ADC a ranar Alhamis, 9 ga watan Afrilu, 2026.
Sanata Marafa ya ce matakin da ya dauka ya biyo bayan wani muhimmin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a jihar Kaduna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
