APC Ta Gamu da Koma Baya, Tsohon Shugabanta Ya Fice daga Jam'iyyar
- Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Jigawa ta gamu da koma baya bayan ficewar wani babban jigo daga cikinta
- Wanda ya fara shugabantar APC a jihar Jigawa, Ado Kiri, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar mai mulki a hukumance
- Ado Kiri ya nuna godiyarsa kan damar da aka ba shi ta ba da irin ta shi gudunmawar a tawon lokacin da ya kasance mamba a jam'iyyar APC
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Jigawa - Shugaban farko na APC mai mulki a jihar Jigawa, Ado Kiri, ya fice daga jam’iyyar a hukumance.
Ado Kiri ya kasance tsohon ɗan majalisar wakilai ne da ya wakilci mazaɓar Ringim/Taura tsakanin 2019 zuwa 2023.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce ya sanar da murabus ɗinsa ne a cikin wata wasiƙa mai dauke da kwanan watan 30 ga Maris, 2026, wadda ya aikawa shugaban mazaɓar Kiri, Malam Salihu Mujtapha.
Meyasa Ado Kiri ya bar APC?
A cikin wasiƙar, tsohon ɗan majalisar ya ce ya ɗauki wannan matakin ne bayan nazari mai zurfi, inda ya ƙara da cewa lokaci ya yi da zai janye daga ayyukan jam’iyyar.
Ya kuma nuna godiyarsa kan damar da aka ba shi na yin hidima da kuma ba da gudunmawa ga jam’iyyar APC a tsawon lokacin da ya yi cikinta.
“Na yanke wannan shawara ne bayan nazari mai zurfi. Ina godiya da damar da aka ba ni na kasancewa ɓangare na jam’iyyar da kuma ba da gudunmawa, gwargwadon ikona, ga ayyukanta da manufofinta a tsawon lokacin kasancewa ta mamba."
- Ado Kiri
Ficewar Ado Kiri ta riga ta fara haifar da martani a tsakanin masu ruwa da tsaki a fannin siyasar jihar Jigawa, la’akari da rawar da ya taka tun farko wajen gina tsarin APC a jihar da kuma tasirin da ya yi gabanin babban zaɓen 2015 da ma bayansa.
Wace jam'iyya zai koma?
Sai dai kuma, murabus ɗin nasa bai nuna aniyarsa ta komawa wata jam’iyyar siyasa ba, lamarin da ya ƙara rura wutar jita-jita game da matakin da zai ɗauka na gaba a harkar siyasa.
Ya kuma bayyana matsayinsa na janyewa gaba ɗaya daga ayyukan jam’iyya, wanda hakan ya bar magoya bayansa da masu ruwa da tsaki cikin rashin tabbas ko wannan matakin hutu ne na siyasa ko kuma wata dabara ce ta daban.

Source: Twitter
Ƙoƙarin tuntuɓar Ado Kiri don samun ƙarin bayani ya ci tura, domin bai amsa kiran da aka yi wa lambar wayarsa ba.
Murabus ɗinsa ya haifar da mahawara a tsakanin masu lura da al'amuran siyasa, inda wasu ke ganin cewa hakan na iya shafar haɗin kan gidan APC da kuma ƙarfin siyasarta a jihar Jigawa gabanin zaɓubbukan nan gaba.
Wani mai suna Ibrahim Manjagara ya sanya wasikar ficewar Ado Kiri daga jam'iyyar APC a shafinsa na Facebook.
APC ta yi magana kan 'yan adawa
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi magana kan rikicin da ya addabi jam'iyyun adawa.
Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida da ke addabar yawancin jam’iyyun adawa alama ce karara da ke nuna ba su shirya rike ragamar shugabancin kasa ba.
Ya bayyana wasu daga cikin rigingimun sun hada da rabuwar kai, shari’o’i, takaddama tsakanin bangarori, da kuma abin da ya kira rashin akida mai karfi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


